Connect with us

KIWON LAFIYA

Muhimman Abubuwa Dangane Da Tafin Kafa

Published

on

Kafafunmu ba karamin muhimmanci ke garesu ba sanin kowa ne sune wadanda suke dauke da nauyin duk wasu sassan mijin mutum, da kafafu ake amfani zuwa duk wasu wuraren da ake so, sune kuma ke dauke da duk nauyin jiki.

Sune kuma ke manya ayyuka masu muhimmanci sai dai kuma , bamu kulawa dasu, mutum na yin duk yadda yaga dama da kafafunshi ba wata damuwa bace.  Duk ta yadda mutum yake son tafiyar dassu ba wani abu bane, wani lokaci ya sa masu safa, wata safar ma  matse su zata yi, ana iya tafiya haka nan ban komai,  dasu kafafun ne, ko ta kan dutse,  da dai sauransu.

Lokacin da ake ta shan wahala musamman ma tafiya kafafu sune masu dauke da wasu abubuwamasu nauyi, ba ma kamar idan aka yi la’akari da tafiyar da ake yi ta rana daya, wani ciwo nan da can a kafafun wannan ma ya isa nuna cewar kafafu ba abubuwan da za’a yi wasa dasu bane. Saboda kuwa suna iya samun matsala ba, wani abin mamaki ba ne.

Ba wai sai mutum ya yi amfani da spa ba wajen kulawa da kafafun shi, saboda shi yana da tsada, idan aka dauki mintuna a rana daya domin a zabi takalmin da yafi dacewa, domin hakan na iya  rage hanyar haduwa da wasu matsalolini da ka iya damuwar su kafafun.

Kafafu masu lafiya sauna da muhimmanci na taimakawa dadi da kuma kasancewa cikin karfi da kuma kuzari, don haka idan ba ‘a kulawa da su ana iya shiga cikinn wasu matsaloli na cututtukan da suka shafi su kafafun. Wannan kuma zai taimaka matuka gaya shiga wani babban taskun da zai samar da ciwo ko ma , har akai ga wata nakasa.

Sai dai kash! Yana da sauki a kula da lafiyar kafafu, ana iya mafani da wadannan shawarwari, domin a kasance, ba a tare da wata matsalar kafafu.

 

1.  A rika kulawa kulawa da kafafu ta wanke su da kuma barin su a bushe, kafafu masu kyau sun fara ne da tsaftace su, ta wankesu da sabulu musamman ma lokacin da mutum yake yin wanka. Bayan haka kuma sai a goge su,  saboda akwai wasu kwayoyin cutar da suke bukatar wuri mai damshi –damshi, wannan zai hana  samu wata matsala. Tsakanin yatsun kafafu sunkamata a kula dasu saboda duk wani ruwa- ruwa ko damshi- damshi, zai iya ba kwayoyin cuta su samu damar kawo wani nakasu, domin  ta hakan kuma sai a samu haduwa da babbar matsala.

2. A duba ko da akwai wasu matsaloli, a kuma samu wata dama akalla sau daya a mako daya, idan akyi wanka,  kamar dai yadda Kurtz ya bada sha lokacin da mutum yake goge jikin shi, idan yazo kan kafafun shi, sai ya lura sosai , ya kuma duba tsakanin ‘yan yatsuntsi shi na kafa koda , akwai wata matsala. Idan an lura da akwa to wannan ya nuna ke nan mutum yana da babbar matsala. Sai kuma a duba akan kunba ko sun canza kala, wannan yana iya nuna da akwai kwayoyin cutar da ake kira nai fungus, idan kuma akwai ciwon siga ya dace mutum ya rika lura da kafafun shi kullun , saboda ita cuta ce mai sa wasu kuraje su fito bisa kafafu.

3.  A rika yanke kunba sosai da kuma fitar da wasu abubuwan da basu kyau, duk wata matsala da aka samu akan kunba, da kuma a bari a yanka kusa da fata, ko kuma su kunbunan ai masu wani abin da zai iya zame ma kafafu matsala, a gaba ta samar da wani ciwo ko kuma cuta.

4.  Kar mutum ya boye kunbar yatsun kafa da bata da kyau, saboda kuma duk kunbar da take da wata kala, ko ta tsage, da kuma wani abin da ba, a saba gani ba, akan kunba ba, wannan yana nuna ke nan da akwai cutar kunba. Idan kuma ka sa wani abu na iya zama matsala.

5.  Mutum yak are kafafun shi wararen da mutane suke, mutum ya tabbar da ya sa wasu takalma, saboda wadannan wurare nan ne ake  haduwa cututtukan da suke samuwa ta kwayoyin cutar fungi.

6.  Kar mutum ya sake har ya rika aron takalmin wani yana sawa, ta hakan yana kamuwa da cutar fungi, har ma safar da wani ya yi amfani da ita, kamar yadda Kurtz ya bada shawara. Wannan ya hada da yin haya, koda yaushe mutum ya kamata ya kula da takalman shi ne yake sawa domin hakan zai sa ya kasance cikin lafiyar kafafun shi.

7.  Kafafun mutum suna da wasu sinadarai da ake kira sweat glands galore, da suka kai 250,000  ko wace kafa, duk wani abin da zai kawo damshi-damshi ko kuma ruwa-ruwa, ire- iren wuraren muhallan da su fungai suke bukata ke nan. Safar da aka  hada da fata tana taimakawa, wajen kawar da duk wani damshi- damshi, da sauri fiye safar da aka yi da auduga, a kuma guji sa safar dake matsewa sosai, don hakn zai iya samar da zufa sosai.

8.  A zabi takalmi mai kyau sosai wato wanda bai matse kafa sosai ba, wannan yana taimakawasu kasance busassu da lafiya, a sa Takalma wadanda aka yi da fata, wannan ya na sa iska ya shiga duk wurin da ya kamata,idan kuma mutum maisaurin yin zufa a kafar shi ne sai ya nemi Takalma wadanda suka dace da shi, domin gudun shiga matsala. A rika sa Takalman da suka dace, wadanda ba sun matsi mutum ba , wato ya kasance tafiyar ma sai tayi wuya. Mutum ya duba Takalman da ba zasu sa kafafun shi kunburi ba, hakana nan ma safar da za’a sa su kasance sun dace da su Takalman. Ya zama ‘yanyatsu zasu samu wurin za’sa rika motsa su.

9.  A gu ji sa Takalma masu tsini wanda zai iya samarwa ‘yanyatsu matsala, har ma kunbuna, idan haka ta samu sai  ayi kokari saduwa da Likita kar mutum ya yi kokarin yi ma kan shi magani, saboda kuwa akwai marasa lafiyar dakin wanka , da suka yi kokarin su yi ma kansu magani a dakin wanka, amma kuma sai suka buge da samun babbar matsala. Duk wani ciwon da aka ji, ko wani jajaja aka gani, ko kuma kunburi, ko kuma an samu canzawar kala, ya dace a samu ganawa da wani kwararre. Idana ka bari Likita ya gani, wannan na iya hana karamar matsala to koma babba.

Idan mutum ya bi wadannan shawarwari goma mutum zai kasance ba zai iya haduwa da wata matsalar, da zata bata ma shi rai dangane da kafa. Saboda zasu kasance ne da inganci ga duk wanda ya yi amfani da su.

 

1.  Mutum ya rika wanke kafafun shi (har tsakanin ‘yan yatsu) tare da auduga a hankali kullun, wannan gaskiya ne, wannan yana nufi ke nan sai mutum ya duka a dakin wanka. Mutum kuma ya yi amfani da sabulu, ko kuma ya zauna kan kujera watakila ma bayan kammala wankan, a wani wuri. A kuma tabbata an wanke kafafun gaba daya tare da su ’yan yatsun, wannan irin lura daza’a yi zai hana kamuwa da cutar athleticfoot, wato yadda kafa take kasancewa da cin ruwa, wari, bacteria, da kuma fungus. Idan kuma ana so asa kafafun ne, ya kamata a manta da gishirin Epsom su wasu sinadarai ne wadanda suke bushewa ne da sauri, ba kuma su bada wani taimakon da zai taimaka wa lafiya. Maimakon haka( kar a yi mafani da ruwam zafi) da kuma dan karamin sabulun ruwa, kamar na wanke kwanoni da ya kunshi da abubuwan da suke  sa fata ta yi taushi.

2.  A shafa ma kafafu wani mai bayan wanke su, lokacin da Fata ke bushewa alal misali watannin dari, idan aka shiga wannan lokaci , da akwai bukatar a rika shafa man sau da yawa a rana. Ba wani mai bane mai tsada da ya wuce lotions da kuma sauran ire- iren man da ake shafawa.

3.  Takalman da mutum zai sa kullun, da akwai bukatar mutum ya kasance mutum yana da a kalla guda biyu, wadanda yafi so, amma kuma Takalma suna bukatar lokaci da kuma iska domin kauce ma kafafun samun matsala kamar ta wani ko kuma wani ciwo. A rika canza safa ko sau daya duk rana, idan kuma da akwai matsala da kafafun da suke wari, sai a sa su cikinwani hadai na binegar da kuma ruwa. Kafafaun ba zasu kawo wata matsala ba. Takalman da suka matse suna kawo matsala, hakanan ma Takalman da suka kasance basu da wani fasali na samarwa kafafu nakasu wajen girma.  Idan kuma ana sa Takalma masu tsawo ne, sai a zabi masu fadi kar kuma su wuce inci biyu. Ya kasance kuma akwai wurin za’a sa ‘yan yatsu, shi ma kasance ada fadi shi ma, idan kuma ‘yan yatsun kafafun mikakku ne, sai a samar da Takalman da suka dace. Shafaffun Takalma basu bada wani taimako, hakanan tafiya hakanan ba bu Takalma. Mata sune aka fi sani da son Takalman dasuke shafaffu wadanda kuma suna taimakawa wajen samun matsalolin kafafu. Saboda a kasance cikin kuzari da lafiya sai a rage sa Takalman da aka san idan aka sa su, ana samun matsala.

4.  Juna biyu, tsufa, da kuma ciwon sigasuna bada matsala akan kafafu. Mata masu juna biyu suna bukatar Takalman da suka fi dacewa dasu, hakanan nauyin da masu ciki ke karawa na samar masu da matsalar, wannan kuma na iya saw a irin Takalman da zasu say a canza, don haka da akwai bukata ta, a gwada kafa. Mata wadanda suka tsufa suna samun raguwar kitse a kafafun su, da bukatar a samu Takalman da suka dace irin yanayi ko halin da ake ciki. Ciwon siga na iya samar damanyan matsalolida zasu damu kafafu da kuma har kasansu. A rika duba ko da akwai matsalolin da kafafu ke fuskanta kullun, ko kuma ganin wani kwararre, a kalla sau daya, a shekara.

 

Muhimman abubuwan sun hada da

A rika duba kafafu kullun

Wanke kafa kullun

Fatar jiki ta kasance da taushi da kuma laushi

Goge duk wasu abubuwan da basu dace ba

Idan mutum zai iya gani tabawa ya kamata a rika yanke kunba akai- akai

Sa Takalma da safa ko wane lokaci

Kare ma kafafu daga zafi ko sanyi

A tabbatar jini na kaiwa da komowa a kafafu

Kafafu wata babbar kafa ce mai lura da duk wata sadarwa tsakanin kasusuwa,ligaments, tendons, da kuma tsokoki.

Idan ana son kafafu su kasance cikin lafiya koda yaushe, saboda sun eke dauke da nauyin jiki. Kafafu suna iya shiga cikin matsala ko kuma wani ciwo. Ciwon kafafu yana iya samar da sauran matsaloli, ma ko wane sashe na kafafun, daga ‘yanyatsu har zuwa duddugen kafafu. Koda yake dai kananan cututtukan da suke damun kafafu ana iya maganinsu a gida, abin na iya daukar lokaci kafin a kawo karshen al’amarin. Likita ya kamata ya dan duba  matsalolin da suka shafi kafafu, bama kamar idan abin ya shafi rauni.

Abubuwan Da Ka Iya Zama Sanadi

Rauni ko amfani fiye da kima ko kuma wani yanayi da ke samar da wani ciwo wanda ya shafi kasusuwa, ko kuma wurin da jijiya ta hadu da jijiya, ko kuma inda kashi ya hadu da kashi, a kafafu hakan yana samar da ciwon kafafu. Ciwon sanyin kashi shi ne babban sanadiyar kamuwa da ciwon kafafu, sai kuma rauni na jijiyoyin kafa na iya kawo wata babbar matsala.

Ciwon sanyin kashi wani babban abu ne mai sanadiyar ciwon kafa, wani rauni  a jijiyoyin kafafu na iya kasancewa sanadiyar ciwo mai zafi sosasi.

Wannan yana iya hadawa da sauran ciwurwukan da suka hada da karyewar dan yatsan kafa, sa Takalman da basu kamata ba, Takalman masu tsawo, ciwon kokon guiwa da dai sauran su.

Sprains da strains wasu raunukan da aka fi yi ne wadanda kuma sun aba tsokar jikin mutum matsala da kuma wurin da kashi da hadu da kashi. Wannan yana faruwa ne idan aka canza wurin  da ake canza inda aka fuskanta ko kuma abin da ake yi. Ko dai a fadi, a kuma sauka ba yadda, ya kamata ba, ko kuma ahadu da wani abu ko mutum, kamar loacin da ake yin wani wasa.

Strain shi ne daya ko fiye da jijiya ta hadu da jijiya ya kasance wani abu ya faru, kamar yagewa ta wurin, strain yana nufin wasu abubuwa ne masu taimakawa tsoka ko dai sun goce ko kuma sun yage, hakanan  kuma ciwo, sprain ko strain yana iya samar da sanadiyar kunburi, ‘yan raunuka, wannan kuma yana iya samar wa mutum ba zai  iya tashi da kan shi ba.

Yawancin ciwurwukan sprains da strains ana iya maganin su a gida ta hanyar amfani da ( kariya, hutawa, amfani da kankara, maganin ciwon jiki).

Gout : Wani ciwo ne na sanyin kashi wanda ake kamuwa da shi ne ta hanyar samuwar uric acid ( wani abin da ya kare amfani) a jijiyoyi, yana kawo zafi mai tsananin gaske, jajaja, da kuma kunburi, sai kuma zafi zafi a wuraren da ya shafi jijiyoyi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: