Mun Gamsu Da Ayyukan Tambuwal A Sakkwato –Bashire

Mun Gamsu Da Ayyukan HONARABUL ABUBAKAR ZAKI BASHIRE shine Shugaban Karamar Hukumar Tambuwal kuma Sakataren Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi a Jihar Sakkwato. A wannan tattaunawar musamman da ya yi da LEADERSHIP A Yau a ofishinsa ya dora Gwamnatin Tambuwal a saman sikeli a mulkin kasa da shekaru uku saman mulki tare da bayyana cewar kwalliya ta biya kudin sabulu. Wakilinmu SHARFADDEEN SIDI UMAR DOGON-DAJI ne ya tattauna da fitaccen dan siyasar.

A matsayinka na Shugaban Karamar Hukuma kuma Sakataren Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi na Jihar Sakkwato ko kun gamsu da ayyukan da ke gudana musamman a yankunan karkara?

Wannan tambayar ta na da matukar muhimmanci. Ka lura dukkanin ayyukan da Gwamnati ke aiwatarwa ta na yi a daukacin Kananan Hukumomi 23 ba tare da fifita wata Karamar Hukuma a kan wata ba domin Kananan Hukumomi sune zuciyar Gwamnati. A daya gefen akwai wasu ayyukan da a ke zabar wani yanki a gudanar. Misali aikin musamman na shirin kiyon shanu da sarrafa madara da ake yi yanzu haka a Rabah wanda shine irinsa na farko mafi girma a bakidaya yankin Afrurka ta Yamma wanda za a kammala a watan Mayu kamar yadda ma’aikatar ta bayyana. Kananan Hukumomin mu 23 suna amfana da mabambantan ayyukan ilimi, kiyon lafiya, samar da ruwan sha, bunkasa aikin gona da sauransu da dama wadanda duka abin yabawa ne. Hasalima a kokarinsa na ganin yankunan karkara sun kara amfana da ayyukan samar da ruwan sha, a yanzu haka an bayar da kwangilar gina tashoshin ruwa masu aiki da hasken rana guda 250 a yankunan karkara. Aikin kamar yadda Gwamnati ta bayyana ya kunshi fanfuna masu aiki da hasken rana, dakin na’ura, wajen rarraba ruwa, bohol da tankin ruwa mai daukar likita dubu 10 tare da zagaye tashar da waya domin tabbatar da tsaro duka wannan da manufar samar da wadataccen ruwa mai kyau ga al’ummar mu.  Bugu da kari an gina Cibiyoyin Koyawa Mata Sana’o’i a bakidaya Kananan Hukumomi 23 da ke wannan Jihar domin bayar da horo na musamman ga mata a sana’o’i daban-daban domin su zamo masu dogaro da kai.

Haka ma a makon jiya ne Mai Girma Gwamna ya kaddamar da aikin karamar tashar samar da hasken wuta mai aiki da hasken rana mai karfin 80kw wanda zai samar da wadatacciyar wuta a garin Kurdula da ke Karamar Hukumar Gudu wadanda gidaje 500 da al’umma dubu hudu za su amfana.

 

Me za ka ce kan shirin daukin gaggawa da Gwamnati ta kaddamar a sha’anin ilimi?

An kaddamar da shirin daukin gaggawa ne domin gudanar da ingantacce kuma sahihin gyara a sha’anin ilimi a wannan Jihar. A kan wannan dalilin ne a kowace shekara Gwamnati ke baiwa fannin ilimi kaso mafi yawa a kasafin kudi. A wannan shekarar ta 2018 sha’anin ilimi ya samu kashi 26.10 cikin 100 wato sama da adadin da Asusun Ilimi na Majalisar Dinkin Duniya ya shata a kebewa ilimi. A shirin an gina sababbin makarantu, an sabunta tsofaffi da dama an kuma samar da kayan aiko da biyan Malamai kan kari. A yanzu haka akwai sababbin Kananan Makarantun Sakandire 86 da za a samarwa al’umma a wannan shekarar da yardar Allah.

Baya ga wannan wani muhimmin abu da za a jinjinawa Gwammati shine karuwar adadin yara masu shiga makaranta da take fadi tashin yi wanda tuni ya haifar da da mai ido domin kuwa Asusun UNICEF ya bayyana cewar an samu karuwar yara masu shiga makaranta daga kashi 69 da suka kauracewa makarantun Furamare a shekarar 2015 zuwa kashi 37 a wannan shekarar. A karshen shekara ba zan manta ba Gwamnatin Jiha ta kaddamar da wani shiri na sanya yara sama da milyan daya makaranta.

Wani abin da zai kara tabbatar maka cewar Gwamnati ta bayar da kulawar musamman a sha’anin ilimi shine gabatar da dokar ‘yancin ilimi ta 2016 wadda ta tilastawa iyaye damar saka ‘ya’yansu makaranta da kuma karfafa masu guiwa domin ganin sun bayar da kulawa ga karatu. Bugu da kari kwanan nan Mai Girma Gwamna ya bayyana cewar Gwamnati za ta yi kawance da Rundunar Sojojin Ruwa domin gina ajujuwan karatu a dukkanin Gundumomi a wannan jiha a shirin musamman wanda kwamitin tuntuba na bunkasa sha’anin ilimi wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar II zai jagoranta. Baya ga wannan akwai shirin musamman na bayar da horo ga Malaman Makarantun Furamare har dubu 3, 374 da manufar ba su ingantaccen horo na kwararru domin su ci-gaba da baiwa al’ummar wannan jiha ilimi mai inganci. A kwanan nan ma dai Gwamnatin Jiha ta mayar da makarantun allo dubu 4, 000 zuwa na zamani da zummar kara adadin yawan daliban da ke shiga makarantar furamare wadanda wasu da dama daga ciki sun fara karatun a baya amma bisa ga wasu matsaloli daya zuwa biyu suka kauracewa makaranta.

A makon da ya gabata a matsayinka na dan jarida ka na matsayin shaidar Gwamnati ta rarraba kujerun makaranta dubu 45, 926 a daukacin Kananan Hukumomi 23 da ke wannan jihar. A can baya a zangon karatu na 2015/2016 Gwamnatin Jiha ta siyo tare da rarraba kujerun makaranta masu zubi biyu ga makarantun Furamare da Sakandire har guda 15, 740. Duka baya ga wannan kuma Gwamnati ta samar da kayan karatu wadanda suka hada da littaffai da kayan koyarwa har dubu 160 ga dukkanin makarantun Gwamnati a wannan Jiha. A fannin biyawa dalibai tallafin karatu a yanzu haka babu dalibin da ke bin Gwamnati bashin tallafin karatu domin a shekarar karatu ta 2016/2017 da ta kare an kashe naira bilyan shida ga biyan tallafin karatu da kudin rajistar karatu ga daliban ciki da wajen kasa. Yanzu haka an bayar da umurnin fara biyan kudin karatu na wannan zangon.

 

Aikin Gona yana daya daga cikin fannonin da Gwamnatin Tarayya ke kiran da a baiwa kulawar musamman domin wadata kasa da abinci. Ko ka na ganin Gwamnatin Tambuwal ta rungumi sha’anin noma da muhimmanci?

Na ji dadin wannan tambayar kwarai da gaske. Domin baya ga rawar gani a fannin ilimi, sashen aikin gona na kan gaba a cikin fannonin da Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta samu gagarumar nasara. Gwamnatin Jiha ta bayar da cikakkiyar kulawa da jajircewa ta musamman wajen bunkasa aikin gona da manufar samar da wadataccen abinci, kawar da fatara da samar da ayyukan yi musamman a tsakanin matasa. A tashin farko an gudanar da aikin tantance manoman asali ba manoman biro ba da manufar sanin ainihin yawan manoma, wadanda za su rika amfana da tallafi da shiraruwan Gwamnati a fannin aikin gona.

A wannan fanni na aikin gona a cikin shekaru biyu kacal Gwamnati ta kirkiro da ayyukan yi har guda dubu 27, 166 a fannin aikin gona kadai. An samar da wadannan ayyukan ne ta hanyar agaji daban-daban domin ci-gaba mai dorewa a fannin aikin gona, ci-gaban yankunan karkara da sauran su. Haka kuma an tallafawa mutane dubu 33 ta hanyoyin bunkasa amfanin gonar da a ke nomawa, tsarin kula da lafiyar dabbobi da kuma tsarin mata da matasa na harkokin gona. Baya ga wannan ga kuma alfanun da manoman mu za su samu a shirin nan na aikin noma wanda aka fi sani da Fadama III wanda aka kiyasta zai lashe tsabar kudi naira bilyan 1.56 a shirin a daukacin Kananan Hukumomi 23 na jiha tare da raba kayayyakin aikin gona da sinadarai ga kungiyoyi 611 a fannin noman shinkafa da tumatur.

Domin kyautatawa manoma da ba su kayan aiki, Gwamnatin Jiha ta siyo injunan ban ruwa har guda dubu 5,000 tare da sayarwa ga manoman shinkafa a kan farashi mai sauki. An siyo kowane injin a kan kudi naira dubu 47 amma an siyar da shi a kan naira dubu 10 kacal. Haka kuma an riga an bayar da iraruwan shinkafa buhu dubu biyar mai nauyin kilogaram 100.

A makon da ya gabata a wannan jaridar na karanta rahoton da kuka wallafa na kaddamar da sayar da takin zamani da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi a sabon kamfanin taki wanda hadin guiwa ne da Gwamnatin Jiha da dan kasuwa mai zaman kansa a inda Gwamnatin Jiha ta sayi takin zamani mota biyu, wato na naira miliyan 104 domin rabawa Kananan Hukumomi 23. Kaddamar da kamfanin ya nuna karara irin jajircewar da Mai Girma Gwamna ke yi wajen bunkasa tattalin arzikin wannna jihar. Duka a fannin aikin gona a yanzu haka Gwamnatin Jiha ta samar da mota 833 ta takin zamani domin noman rani na wannan shekarar. A kan wannan an kashe tsabar kudi naira bilyan 3.4 domin sayen taki wanda za a rarrabawa manoma kan farashi mai rahusa.

 

Ko akwai wani yankuri da Gwamnati ke yi domin daga darajar kananan asibitoci zuwa manya domin bayar da kaimi wajen shawo kan matsalolin kiyon lafiya?

Daga darajar kananan asibitoci aiki ne da a ka yi kuma cikin nasara. Da farko ba zan manta ba, a watan Mayu 2017, Gwamnatin Jiha ta sanya hannu kan wata yarjejeniya ta naira bilyan 2.8 kan wani tsari na shekara daya da Asusun Kula Da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) Tsarin zai shafi fannoni masu muhimmanci na kiyon lafiya, ilimi da kuma tsaftace ruwa. Zan baka misali a karkashin kiyon lafiya, wato Gwamnatin Jiha kamar sauran fannoni ta fito da hanyoyi na samar da kwararru 33 domin tattaunawa kan kundin tsarin inganta kiyon lafiya na Jihar Sakkwato daga 2016- 2020. A cikin wannan tsarin a yanzu haka Manyan Asibitoci shida sun samu ci-gaba ta hanyar daga darajar su daga Kananan Asibitoci zuwa Manya wato General Hospitals. Haka kuma Gwamnatin Jiha ta kaddamar da shirin hadin guiwa na kiyon lafiya wanda Gwamnati ta zuba tsabar kudi naira milyan 100 domin amfanin al’ummar wannan jiha bakidaya. Baya ga wannan a yanzu haka idan ka je Asibitin Kwararru za ka ga yadda a ka samar da kayan aiki na zamani baya ga magani kyauta da a ke baiwa mata masu juna biyu da kananan yara ‘yan kasa da shekaru shida.

Yanzu haka dukkanin Cibiyoyin Kiyon Lafiya a Matakin Farko a Kananan Hukumomi 23 an mayar da su a karkashin inuwa daya domin tafiyar da lamurra bai daya. Haka kuma Gwamnati ta na samun nasara a shirin ceton lafiyar al’umma miliyan daya wanda a ke kira Lafiya Leka Gidan Kowa da nufin kula da lafiyar al’umma har a bakin kofar gidajen su. Duka a fannin lafiya an kara inganta ayyukan Hukumar Yaki da Cutar Malariya domin kawar da cutar bakidaya a Birni da Karkara a bisa ga illar da take da shi da dai sauran abubuwa da dama da Gwamnati ke yi a dukkanin fannoni domin sauke nauyin da al’umma suka dora mata ciki kuwa har da biyan fansho na naira bilyan shida ga Ma’aikatan Kananan Hukumomi da Malaman Furamare.

 

Exit mobile version