Muhammad Maitela" />

Mun Gyara Hanyoyin Karkara Don Saukaka Radadin Boko Haram – Kwamishinan Ayyukan Yobe

Gwamnatin Jihar Yobe ta bayyana cewa, ta samar da hanyoyin mota a yankunan karkara tare da gyara wasu a bangarorin jihar daban-daban, domin saukaka yanayin mawuyacin halin matsalar rikicin Boko Haram ga al’ummar jihar.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin kwamishina a ma’aikatar ayyuka a jihar Yobe, Injiniya Umar Duddaye, a takardar manema labarai, ranar Laraba, a jihar.
Bugu da kari, Injiniya Duddaye ya ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen aiwatar da manyan ayyukan ci gaba, musamman ta fannin shimfida hanyoyin mota da magudanun ruwa a birni da karkara a fadin jihar.
Ya kara da cewa, jihar ta gina hanya mai tsawon 4km da magudanun ruwa ma su tsawon 8km a garin Buni Yadi; hanya 1.6km tare da magudanun ruwa 3.2km a garin Damagum, hadi da hanya 1.5km da magudanun ruwa 3km a garin Babban Gida a jihar.
Har wala yau, ya kara da cewa, “Baya ga wadannan, gwamnatin jihar ta gina hanya mai tsawon 2.3km da magudanun ruwa 4.6km a garin Jaji-Maji, hanyar 1.0km tare da magudanun ruwa 2.0km a unguwar Mallum Mattari da karin wata hanya mai tsawon mita 800 da magudanun ruwa a rukunin gidaje a ma’aikatar ayyuka da ke birnin Damaturu.”
Sauran hanyoyin, wadamda aikin su ke gudana sun kunshi hanya mai tazarar kilomita 16 daga Nguru zuwa Balanguwa, hanya 12km daga Damagum zuwa Gubana, gina hanya mai tazarar 2.6km hadi da magudanun ruwa 5.2Km a garin Potiskum.
A hannu guda kuma, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta biya yan kwangila ilahirin kudaden ayyukan da ke gudana da ta gada, wadanda suka hada da tagwayen hanya 25.5Km daga birnin Damaturu zuwa Kalallawa, tagwayen hanya 4.5Km wadda ta tashi daga sha-tale-talen kwata zuwa New Bypass.

Exit mobile version