Muhammad Shafi’u Saleh" />

Mun Kammala Shirye-Shiryen Gudanar Da Zabe -INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ce ta kammala daukacin shirye-shiryen gudanar da zaben kujerar shugaban kasa, da zai gudana ranar asabar mai zuwa.
Da yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a harkokin zabe a jihar Adamawa Kwamishinan hukumar zabe a jihar Adamawa Baresta Kassim Gaidam, ya ce hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da ingantaccen zabe a jihar.
Gaidam ya ci gabada cewa “ta ko wani bangare hukumar INEC ta kammala shirye-shiryen da ya kamata ta yi, domin gudanar da ingantaccen zaben shugaban kasa a jihar Adamawa.
“kawo yanzu mun amshi katin zabe na masu kada kuri’a 2, 024884, a jihar Adamawa, daga ciki 1, 788,706 ake sarar zasuyi zabe azubukan shugaban kasa na ranar asabar.
“INEC ta bada horo ga ma’aikatan wucin-gadi da shirya malaman zabe dama jami’an tsaro da zasuyi aiki a rumfunan zabe 4104, da mu ke da su a jihar Adamawa” inji Gaidam.
Da yake magana game da raba kayan aikin zabe kuwa shugaban hukumar zabe ta jihar Kassim Gaidam, ya ce “ranar juma’a zamu rarraba kayan aikin zabe da’aka adanasu a rassan babban bankin Nijeriya, mun adanasu a gaban wakilai na jam’iyyu daban daban.
“Ranar asabar da misalin 8 na safe, ma’aikatanmu zasu bude rumfunar kada kuri’u domin gudanar da zabe a fadin jihar” inji shi.
Da shima ke jawabi a taron kwamishinan ‘yan sandan jihar! Muhammad Garba Mukaddas, ya ce jami’an tsaro sun kammala duk shirye-shiryen da ya kamata domin tabbatar da tsaro yayin gudanar da zabe dama bayan zaben.
Haka kuma kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci jama’ar jihar da sukasance masu bin doka da oda, musamman da yake an shaidesu da zaman lafiya.
Wakilan jam’iyyu daban daban da suka halarci taron sun gabatar da jawabai a lokacin taron, sun kuma yi kira ga hukumar zabe da jami’an tsaro na ganin zaben ya gudana bisa gaskiya da adalci a zaben.

Exit mobile version