Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gode wa ministocinsa da ma’aikatan fadar shugaban kasa da suka yi aiki tare da shi cikin shekaru takwas da suka gabata.
Shugaban kasar wanda zai mika wa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayu, ya ce yana alfahari da cewa shi da mukarrabansa sun bai ‘yan Nijeriya iya gudunmawarsu.
- Tabbas Za’a Karyata Jita-Jitar Dake Shafawa Jihar Tibet Bakin Fenti
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 96 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Kano
A taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) da aka gudanar a zauren majalisar dokoki, shugaban ya mika godiyarsa ga dukkanin ministocin bisa jajircewar da suka yi wajen cimma manufofin gwamnatin, inda ya bukaci a marawa shugaban kasa mai jiran gado baya.
“Ina alfahari da cewa mun yi iya Kokarinmu,” an ruwaito shugaban kasar yana fadar haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar.
Shugaban ya umarci ministocin da su gyara ayyukansu tare da kaucewa gaggawar da ka iya kawo cikas ga ayyukan alheri da suka yi tsawon shekaru.
“Sakamakon shekarun da muka yi tare, tsawon shekaru bakwai da rabi, mun bambanta kan batutuwa da yawa. Ina rokon mu fahimci cewa wadannan mukamai sun kasance na gama gari ne, kuma babu wanda ya isa ya ci gaba da koke-koke, ko ci gaba da wadannan bambance-bambance.
“Ga wadanda ba za su kasance cikin gwamnati kai tsaye ba, na san ina daya daga cikin irin wadannan, ina rokon mu ci gaba da bayar da goyon bayanmu, ta kowace hanya, idan babbar jam’iyyarmu ta kira mu, wacce ta ba mu damar tsayawa, kuma dole ne mu ci gaba da mara mata baya ta kowace hanya da za mu iya,” in ji shi.
Shugaban ya danganta duk wani kyakkyawan aiki da fatan alheri da gwamnatin ta samu da taimakon Allah, inda ya kara da cewa, “Ina kuma gode wa Allah da Ya ba mu karfin gwiwa da ya hada mu baki daya.
“Zan kuma yi farin cikin yin abubuwa da dama da ban samu ba tun ranar 29 ga watan Mayu, 2015, daya daga cikin irin wannan shi ne lokacin da na fi so na kula da shanuna.
“Ina yi mana fatan alheri kuma ina fatan mu ji labari mai dadi a duk lokacin da aka ambaci sunayenmu. Na gode kuma Allah ya albarkaci Tarayyar Nijeriya,” in ji shi.