Connect with us

WASANNI

Muna Bukatar Mu Cika Alkawarin Da Muka Daukar Wa Magoya Baya

Published

on

Tottenham ta kawo karshen doke ta da ake yi sau uku a jere a wasa inda ta yi nasara 2-1 a gidan Brighton a wasan Firimiya na mako na shida, ta zama ta biyar a teburin gasar a wannan satin.

Tottenham  ce ta mamaye wasan wanda aka sha ruwan sama sosai a lokacinsa a filin East Sussed, inda Harry Kane ya karya alkadarin Brighton a minti na 42 ya ci fanaretin da alkalin wasan ya bayar saboda Glenn Murray ya taba kwallo da hannu.

Anthony Knockaert ya barar wa da masu masaukin bakin damar farke kwallon a minti na 66, inda ya sheka kwallon kai tsaye zuwa golan Tottenham Paulo Gazzaniga.

Erik Lamela ya ci wa Tottenham kwallo ta biyu a minti na 72, amma kuma Knockaert ya rama wa Brighton daya bayan minti 90 da doriya na wasan.

Sakamakon ya sa Tottenham ta zama ta biyar a tebur da maki 12 a wasa shida, yayin da Brighton ta zama ta ta 13 da maki biyar.

“Munsha wahala a kwanakin baya saboda munyi rashin nasara a wasanni uku, biyu a firimiya daya kuma a gasar zakarun turai saboda haka muna bukatar samun nasara domin ganin mun dawo hayyacinmu”. In ji kociyan kungiyar

A karshe yayi kira ga ‘yan wasan kungiyar dasu sake dagewa da samun nasara domin ganin sun cimma burin da suka daukarwa magoya bayansu a wannan kakar na lashe kofi.
Advertisement

labarai