Muna Da Kyakkyawar Fahimtar Juna Da Sauran Kabilu A Legas – Amadu Mai-Mai

Mai-mai

Daga Bala Kukkuru,

Shugaban kungiyar rukunin masu kasuwancin man gyada dake kasuwar Mile-12 Intanashinal Market na Jihar Legas, kuma dan asalin unguwar Kofar Ruwa da ke karamar hukumar Dala a cikin Jihar Kano, Alhaji Ahmadu Mai-Mai, ya bayyana cewa, akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakanin al ‘ummar Hausawa da sauran kabilu mazauna Jihar Legas.

Alhaji Mai-Mai ya yi wannan tsokaci ne a gidansa da ke unguwar Kofar Ruwa a cikin garin Kano Jim kadan bayan kammala taron addu’ar daurin auren diyarsa mai suna Rabiatu Alhaji Amadu mai mile12 da angonta Surajo Sani Jafar Kano, tare da gudanar da addu’ar neman amincin Allah ga cigaba da samr da zaman lafiya a Nijeriya tare da kwantar da dukkan fitintinu da ke tasowa a kasar nan baki daya.

Taron addu’o’in guda biyu wanda ya samu halartar manyan malamai da suka fito daga sassa daban-daban da ke cikin jihar kano da Kaduna, da malaman yarbawa da nufawa wadanda suma suka fito daga jihar legas da sauran al’umma baki daya a ranar lahadin da ta gabata. Alhaji Ahmadu ya ce, fadin albar kacin bakinsa bisa dalilin da ya sanya ya kira taron gudanar da addu’o’in shine ne domin gabatar da daurin auren diyarsa mai suna Rabiatu da mijin ta Surajo Sani Jafar Kano da gudanar da addu’o’in nemar wa kasar nan karin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar baki daya.

Ya kara da cewa, don haka ya ga ya zama wajibi ga malaman arewacin Nijeriya da ‘yan kasuwa da sauran al’umma da su ci gaba da gudanar da irin wadannan addu’o’in na musamman domin neman yardar uban giji wajkn kare dukkanin matsalolin tsaro ya yi wa kasar nan kawanya kuma yake yi ma ta barazana a halin yanzu. YA kuma isar da sakon godiyarsa wajen malamai da sauran al’ummar da suka fito daga sassa daban-daban na kasar nan suka shigowa legas domin tayashi murnar gudanar da taron addu’o’in guda biyu, wanda da fatan Allah ya saka masu da alheri.

Shima a nasa tsokacin bayan kammala addu’a daga cikin mahalarta taron kuma uba ga Alhaji Amadu mai kasuwar ‘mile12 Intanashinal market’ tsohon Shugaban kasuwar ta ‘mile I2’ kuma Shugaban kungiyar amintattun Dattawan kasuwar Alhaji isa Mohammed mai shinkafa mile12, ya bayyana cewa, babu shakka wajibine ga al’ummar arewacin Nijeriya da su cigaba da gudanar da Irin wadannan addu’o’in domin kawar da miyagun aiyuka ta’addanci wadanda suke faruwa a cikin wasu jihohin arewacin Nijeriya a halin yanzu, da fatan Allah uban giji ya shige mana gaba a kan wannan al’amari sannan, kuma ya ummurci al’ummar Hausawan kasuwar ‘mile12 Intanashinal market’ dasu cigaba da hada kawunansu da juna a kowanne lokaci tare da bin dokokin kasuwar domin samun nasarorin kasuwancin su dana rayuwar su ta yau da kullum. Sauran jawaban da suka fito daga bakunan malamai da sauran al’umma a wajen taron gudanar da addu’o’in guda biyu sun yi kira ga al’umma baki daya dasu ci gaba da gudanar da irin wadannan addu’o’in domin karin samun zaman lafiya a kasar nan baki daya.

Exit mobile version