Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Muna Fatan Rabuwa Da Ozil -Arteta

by Muhammad
January 9, 2021
in WASANNI
3 min read
Ozil Arteta
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta ya ce kofa a bude take ga dan wasan gaban kunagiyar, Mesut Ozil ya bar kungiyar a wannan watan, bayan rike dan wasan Jamus din tare da kin sanya shi cikin jerin ‘yan wasansa na wannan kakar.

Duk da cewa ya fi kowa yawan daukar kudi a kungiyar, amma wasa daya kawai ya buga mata na 1-0 da ta yi nasara kan West Ham a ranar 7 ga watan Maris din shekarar data gabata lokacin da aka koma hutu bayan vullar cutar Korona.

samndaads

Dan wasan dan shekara 32 a duniya yana da sauran watannni shida a kungiyar a kwantaraginsa, kuma yana da damar tattaunawa da wasu kungiyoyin domin komawa kyauta bayan karewar kwantiraginsa a kakar wasa mai zuwa.

Hakan dai zai kawo karshen zamansa na shekara takwas da ya kwashe a Landan a makwanni masu zuwa, ya yin da wasu rahotanni daga Turkiyya ke cewa ya fara tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta  Fenebahche.

Ya ci gaba da cewa “In mun cimma wani abu a wannan wata zai fi yi wa kowa dadi, zai yi wa Ozil dadi a rayuwarsa ta gaba, kuma zai fi yi wa Arsenal dadi saboda haka muna kan tattauna abinda yakamata ayi”.

Dan kwallon wanda baya cikin ‘yan wasa 25 da ke buga wa Arsenal wasannin Premier League da Europa League a bana, ya koma kungiyar da buga wasa a matakin mafi tsada a kungiyar kan kudi fam miliyan 42.4 a shekarar 2013 daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Rabonda ya buga wa Arsenal wasa tun ranar 7 ga watan Maris kuma kocin Arsenal ya tabbatar da cewar Ozil na yin atisaye da sauran ‘yan wasa, amma an bashi hutu ne bisa wani batun da ya shafe shi a baya.

A satin da ya gabata ne kociyan na Arsenal, Mikel Arteta, ya tabbatar da shirin kungiyar na sallamar ‘yan wasa bayan an bude kasuwar hada-hadar sauyin shekar ‘yan wasa a ranar Juma’ar satin daya gabata.

Artrta, ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a daren Asabar, dangane da shirinsu na ganin sun kara katfin tawagar ta hanyar sayar da wasu daga cikin ‘yan wasan da basa bugawa kungiyar wasa domin sayo wadanda zasu taimaka wajen ci gaban kungiyar.

Arteta ya ce aniyarsa a yanzu ita ce rage yawan ‘yan wasan dake tawagarsa ta farko domin dai-daita tsarin aiwatar da dabarunsa na kai kungiyar ta Arsenal ga gaci, sai dai bai bayyana sunayen ‘yan wasan da yake shirin sallama ba, amma kuma wasu majiyoyin na ganin ba za su wuce, Mesut Ozil, Kolasinac da callum Chambers ba.

Sai dai shima Arteta yana fatan kungiyar zata fitar da kudi domin sayo sababbin ‘yan wasan da zasu taimakawa kungiyar a kokarin da kungiyar take yin a farfadowa daga koma bayan data samu a watannin baya.

Tuni daman ake danganta Arsenal da sayan dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Isco, wanda baya samun damar buga wasa a cikin tawagar ta Zidane sai dai Arsenal aro take bukata ta dauka zuwa karshen kakar wasa idan yayi abin kirki sai ta saya.

Ana fatan dai shugabannin kungiyar ta Arsenal zasu hoyawa Arteta baya da kudi a wannan watan domin sayan sababbin ‘yan wasan da zasu taimakawa kungiyar cimma burinta na wannan shekarar na zuwa kofin zakarun turai.

SendShareTweetShare
Previous Post

Karim Benzema Zai Gurfana A Gaban Kotu Bisa Zargin Cin Amana

Next Post

Amfanin Ruwan Kokwamba A Jikin Dan’adam

RelatedPosts

Arteta

Ya Kamata Mu Dora Daga Nasarar Da Muka Samu Kan Newcastle – Arteta

by Sulaiman Ibrahim
11 hours ago
0

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta karbi bakuncin kungiyar Newcastle...

Kociyan Bilbao

Messi Ya Yi Kuskure A Matsayinsa Na Babba – Kociyan Bilbao

by Sulaiman Ibrahim
11 hours ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Athletico Bilbao, Marcelino Garcia, ya...

Allison

Klopp Ya Jinjina Wa Allison Bayan Wasan Manchester

by Sulaiman Ibrahim
11 hours ago
0

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool,...

Next Post
Kokwamba

Amfanin Ruwan Kokwamba A Jikin Dan’adam

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version