Musulmin Kudu Maso Gabas,a karkashin inuwar Kungiyar Da’awah ta Musulmin Igbo, za ta kaddamar da Alkur’ani mai tsarki da aka fassara da harshen Igbo a ranar Juma’a.
Kungiyar ta bayyana haka ne yayin zantawarta da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.
- Zargi Safara: Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Lauyoyin Da Za Su Je Burtaniya Don Kare Ekweremadu
- Ukraine Na Bukatar Dala Biliyan Biyar Domin Yakar Rasha A Kowanne Wata
Wakilan kungiyar karkashin jagorancin Muhammed Muritala Chukwuemeka, sun ce shi da tawagarsa sun yanke shawarar isar da sakon Allah ga ‘yan’uwansu Igbo ta hanyar Alkur’anin da aka fassara da yarensu.
A cewar rahoton, Chukwuemeka, dan asalin Karamar Hukumar Orlu ta Jihar Imo, ya bayyana addinin musulunci a matsayin addinin zaman lafiya da ya haramta kashe dan Adam, inda ya kara da cewa aikin fassarar ya dauki kusan shekaru biyar kafin ya kammala.
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su halarci taron kaddamar da bikin, wanda za a yi bayan sallar Juma’a a masallacin Ansar-ud-deen da ke Maitama, a birnin tarayya Abuja.
Chukwuemeka, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya masu kishin kasa da su tallafa wajen samar da littafi mai tsarki domin isar da sakon Allah cikin lumana ga ’yan kabilar Igbo a Kudu Maso Gabas da sauran sassan Nijeriya.
“Kasa da shekara biyar ba kafin na kammala fassarar. Muna kira ga ’yan Nijeriya masu hannu da shuni da su taimakawa wajen samar da littafi mai tsarki da yawa. A yanzu haka mun buga kwafi 500 kuma an riga an tura kwafi 100 zuwa Kudu Naso Gabas,” inji shi.