A kalla mutum 52 ne suka tsallake rijiya da baya a wani hatsarin da ya rutsa da motoci shida a kan titin Ihiala, karamar hukumar Ihiala da ke Anambra yayin da Sabuwar Shekarar 2021 ta fara ranar Juma’a.
Mista Andrew Kumapayi, Kwamandan jihar, na Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC), ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Awka.
Kumapayi ya ce hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 2 na dare ya faru ne sakamakon saurin gudu da rashin kulawa.
“Hadarin da yawa ya shafi motar Toyota Hiace mai lamba AGB268ZT, da Mark Tireka mai lamba GWA456YR da kuma wata motar Toyota Hiace mai lamba NEN106DK. Kwamandan ya ce wani rahoton shaidu da ya kai ga FRSC ya nuna cewa direban daya daga cikin motocin yana gudu, sai ya rasa yadda zai yi da motar sannan ya fada cikin sauran motocin guda biyar.