Connect with us

KIWON LAFIYA

Mutum Sama Da Miliyan Uku Barasa Ke Kashewa Duk Shekara –WHO

Published

on

A wani rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar ranar Jumma’a ya nuna cewar fiye da mutane milyan uku ne suke mutuwa ko wacce shekara kamar dai wani rahoto na shekarar 2016 ya nuna, a sanadiyar matsalar shan barasa, kamar dai yadda rahoton ya nuna wanda aka yi ma lakabi da “Rahoton duniya dangane da shan barasa da kuma lafiya na 2018 “ daya daga cikin wacce mutuwa wanda kuma shi ne ya kunshi 1 a ko wacce mutuwa 20.

Wani abu kuma gaba daya babbar matsalar amfani da barasa a sanadiyar haka ake samun mutuwar kashi 5, dangane da babbar matsalat da cutar take samarwa a duniya.

Rahoton ya nuna cewar dangane da mutuwar da ake sam fiye da daya bisa uku maza ne.

Akan dukkan mace macen da ake yi dangen da shan giya, kashi 28 a sanadiyar raunuka ne, wato kamar haduran da suka shafii tukin mota da kuma, yadda mutum zai cutar da kan shi da kuma al’amarin daya shafi fadace fadace.

Hakanan ma kashi 21 abin ya shafi al’amarin daya shafi matsalolin yadda jiki yake sarrafa abinci, da kuma kashi 19 na cardiobascular disease, sauran kuma saboda wasu matsalolin cututtukan, kansa, al’amarin daya shafi cutar hauka, da kuma wasu sauran matsaloli na lafiya.

Duk da wadannan matsalolin da suke sanadiyar mutuwa saboda shan giya, da kuma wasu  abubuwan da suke da alaka da mace macen da aka yi shekara ta 2010, babbar matsalar cutar da kuma raunukan, wanda  dalilin amfani da giya.

Wannan abin an fi samun shi bangaren Europe da kuma Amurka kamar dai yadda rahoton ya nuna.

Bugu da kari kuma a duniya an kiyasata cewar akwai maza milyan 237 da kuma mata 46, wanda suke fama da matsalololin da suke da nasaba da shan giya.

An kuma fi samun ita wannan matsalar tasaknin maza da mata a bangaren Europe dake da (kashi 14.8 da kuma kashi 3.5) sai kuma sashen Amurka (kashi 11.5 da kuma 5.1) matsalar amfani da giya ko kuma barasa, an fisamun wannan al’amari a kasashen da al’ummarsu suke samun kudaden shiga masu yawa.

Rahoton ya nuna cewar ana iya samun karuwar amsu shan giya nan da shekaru goma masu zuwa.

Sai dai kuma ko irin yawan ita giyar da ake sha a kullun,an kiyasta cewar ana shan giram 33 na ainihin giyar kon wacce rana.

Wannan yana nuna ke nan abin ya kai ga gilas (wadanda suke 150 ml) na giya babbar kwalba (750ml) na kwalbar giya wadda za a iya shan sau bitu (ko wacce tana da 40ml)..

Gaba daya a duniya fiye da daya bisa hudu wato kwata ke nan ko kuma (kashi 27) na masu shekaru 15 zuwa 19 duk mashaya giya ne.

Har ila yau rahoton ya nuna akan yadda ake shan giya yanzu a bangaren Europe shekaru 15 zuwa 19 sne suka fi kowa shan giya wanda kuma shi ne (kashi 44) sai kuma nahiyar Amurka mai (kashi38) ga kuma sashen pacific ta yamma mai  (kashi38).

Sabeya n makaranta ya nuna cewar a kasashe masu yawa amfani da giya ya fara ne daga shekaru15, abin kuma da akwai bambance bambance tsakanin yara maza da kuma yara mata.

A fadin duniya kashi 45 na wadanda aka sani suna shan giya a matsayinta na spirit beer ita ce ta biyu, wadda ake ganin ita ce giya ta ainihi shi ne  (kashi 34) sai kuma wine wanda suka kasance kashi 12) ne.

Rahoton dai ya yi kira ga bukatar kara samun kasashe wadanda za su dauki mataki dangane da daukar wani mataki akan matsalar da shan giya ke samarwa.

“ Mutane da yawa su da iyalan sa da kuma al’ummarsu sune za su shiga matsala danagane da shan giya, ta hanyar tashe tashen hankula, samun raunuka, ga kuma matsalolin da suke da dangantaka hauka da kuma cututtuka kamar kansa da kuma mutuwar bangaren jiki.

“Lokaci ya yi wanda ya kamata a dauki mataki saboda a kawo karshen wannan babbar matsalar dake damuwar al’umma”.

“ Akwai bukatar a ga cewar su kasashen da suke cikin kungiyar su yi kokarin samo yadda za a gane bakin zaren, saboda a ceto rayukan mutane, kamar sa haraji akan giya, da kuma tsagaita tallace tallacen giya”.

“ Ya kamata a dauki wasu matakai na wani tsaikon da ake son cimmawa wadanda gwamnati ta sa, da suka hada da rage shan giya da kashi 10 a duniya baki daya, tsakanin shekarar 2010 da kuma 2025” kamar dai yadda Tendos Adhanom Ghebreyesus wanda shi ne babban jami’in na hukumar lafiya ta duniya.

“Matakan da za a dauka sun hada da kara haraji akan sigari, hana tallar giya, sai kuma hana yadda za a iya samun giya ba tare da wata matsala ba”. Kamar dai yadda Mista Poznyak ya bayyana.

annobar tarin fuka.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: