Connect with us

SIYASA

Na Fito Neman Gwamnan Bauchi Ne Don Gyara Barnar Da Gwanatin APC – Abdul Ningi

Published

on

Dan takarar gwamnan Jihar Bauchi a karkashin tutar jam’iyyar PDP Sanata Abdul Ahmed Ningi ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi domin ceto Jihar daga kuncin talauci da barnar da jam’iyyar APC a karkashin gwamnatin Mohammed Abdullahi Abubakar ta yi wa Jihar tun daga lokacin da suka kama mulki,  al’amarin da ya bayyana cewa ya mayar da Jihar Bauchi baya sosai inda a halin yanzu ake ikiririn ita ce Jihar da ta fi kowacce fama da talauci a fadin Nijeriya.

Abdul Ningi ya bayyana haka ne a lokacin da ya ayyana niyyar sa ta tsayawa takarar gwamna a harabar sakatariyar jam’iyyar PDP ta Jihar Bauchi cikin wannan makon,  inda ya bayyana cewa an shiga mawuyacin hali saboda ganin yadda wannan gwamnati ta rike komai ta hana mutane hakkokinsu na kudin barin aiki da albashin da doka ta tanada da kuma kin daukar ma’aikata da bayar da kwangilolin bogi da sauran ayyukan almundahana da wannan gwamnati ta APC ke aiwatarwa yadda gwamnan ya mayar da mutanen Jihar Bauchi tamkar bayi.

Ya ce abin mamaki ne yadda gwamna ke zama a Abuja yana kasafin kudin Jihar Bauchi ya hana kananan hukumomi hakkokin su na aiki babu kuma wani aiki da ake yi musu, don haka idan ya samu mulkin Jiha zai mayar da kowace kwangila hannun mutanen kowace karamar hukuma ta yadda arziki da ingancin aiki zai dawo. Kuma a shirye yake wajen ganin ya dauki ma’aikata don a raba matasa da zaman kashe wando. Ya ce an wayi gari hukumomin gwamnati sun lalace babu ma’aikata, hatta gine-ginen gwamnati da iska ta lalata wannan gwamnati ta gaza gyarawa komai sai lalacewa yake yi saboda sakacin wannan gwamnati a Jihar Bauchi. Don haka ya ce ba za su yarda a ci gaba da lalata wannan Jiha baki sun zamo ‘yan kwangilar kashe mu raba an bar mutanen jiha a talauci.

Sanata Abdul Ningi cikin jawabinsa ya bayyana cewa mutane da yawa sun bar wannan jam’iyya ta PDP a baya saboda ganin ba a musu adalci amma yanzu suna dawowa saboda jam’iyya tana nan daram ba wanda zai ga bayan ta saiko duk wanda bashi da gaskiya ta ga bayansa, kuma sun gamsu a yanzu APC ta zarta PDP rashin adalci da neman kashe mutane da wahala.

Suna nan daram ba yadda za su je har sai  sun dawo da martabar PDP a Nijeriya kuma dama rashin adalci ya sa wasu suka bar jam’iyyar suka je inda aka fi PDP rashin adalci yanzu kuma suke dawowa cikin PDP don a hadu a ceto wannan kasa daga talaucin da ya lalata kasa da mutanen ta.

Abdul Ningi ya kara da cewa kowa ya sani Allah ya ce tashi na taimake ka, don haka yadda mutane suka tashi a wancan lokaci ya kamata a yanzu su sake tashi don a ceto wannan kasa daga halin da ta shiga na wahala saboda mulki na Allah ne kuma yana bayar da shi ga duk wanda yake so.

Don haka ya ce bai  fito neman gwamna don garin su Ningi ba ne ya fitone don ceto Jihar Bauchi gaba daya a hadu a gina jiha a gyara barnar da masu mulkin wannan lokaci suka wanzar a wannan lokacin.

Ya ce bai fito wannan takara ba sai da ya tuntubi mutane kuma suka yi na’am, don haka yake ci gaba da neman goyon bayan jama’a don a ceto jihar ta hakane za a kawo gyara daga barnar da APC ta yi wa Jihar Bauchi da kananan hukumomi da mutanen jiha don a fita daga mawuyacin halin da aka shiga na izzar masu mulkin wannan lokaci.

Shi ma a nasa jawabin Alhaji Hamza Kwoshe Akuyam shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi a lokacin da ya ke amsar tawagar Sanata Abdul Ahmed Ningi ya bayyana wannan tafiya a matsayin tafiyar masu kishin Jihar Bauchi, kuma tafiya ce wadda ta samu goyon bayan manyan mutane don haka suma suke marhabin da wannan tafiya. Inda ya kara da cewa Sanata Abdul Ningi yana cikin jam’iyyar PDP tunda aka kafata har ta hau mulki a 1999 bai taba gusawa ko ina ba, kuma ya rike madafun iko da shugabancin kwamitoci dabam dabam a majalisar dattawa da ta wakilai a tarayya.

Abba Akuyam ya kara da cewa kowa ya san rawar da Sanata Abdul ya taka wajen gina mutane a Jihar Bauchi da kasa baki daya, don haka a shirye wannan jam’iyyar take wajen ganin ta goyawa duk wanda ke son kawo ci gaba baya, saboda haka ya ja hankalin ‘yan jam’iyyar da mutanen Jihar Bauchi da su rika lura da irin ci gaban da kowane mutum ya kawo kafin su zabe shi a kan kowane matsayi.

Shima Darakta Kamfen na Sanata Abdul Ahmed Ningi, Alhaji Maijama’a Mohammed Bununu cikin jawabinsa ya ja hankalin jama’a kan su lura da matsayin Sanata Abdul Ningi game da gudummowar da ya bayar a majalisun tarayya don haka ya kamata mutane su zamanto masu kishin kansu da kishin wadanda ke kiyaye musu hakkokinsu don ciyar da su gaba. Ta haka ne za a dawo da walwala da ci gaban da masu mulkin wannan lokaci suka lalata a kasar nan. Don haka ya shawarci jama’a da su lura da masu son su na gaskiya  su gujewa masu farfaganda suna cutar da su suna cutar da kasa da sunan canji amma sun bar mutane suna wahala su kuma sun kwashe iyalensu sun tura kasashen waje da nufin basu san me zai auku ba a siyasa mai
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: