Daga Ibrahim Muhammad,
Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Hon. Alhaji Sani Mukaddas, Barden Bichi ya bayyana cewa a matsayinsa na zababben shugaba a Karo na biyu da yake daf da kammala wa’adin mulkinsa, Allah ya cika masa burin da ya ke da shi na son ya ga kafin ya bar ofis a kammala ginin sabuwar mayankar garin Bichi, wacce ya assasa da yanzu haka kuma cikin ikon Allan ya nufa an kammala ginin.
Ya ce Mahankar za ta taimaka wa Karamar Hukumar sosai wajen samar da aikin yi da kuma nama mai tsafta don inganta lafiya da rayuwar al’umma da habaka tattalin arzikin yankin.
Hon. Sani Mukaddas ya ce wannan aiki na mayanka da aka yi sabo, doru ne akan irin dimbin ayyuka da aka rika yi a shugabancinsa a fannoni daban daban, duk da halin da aka sami kai a kasar nan na matsalar koma-bayan tattalin arziki da ya sa abubuwa ba su tafi yadda ake so ba. Sannan kuma sai ga annobar da addabi Duniya baki daya.
Ya kuma bayyana nagartat al’ummar Bichi da cewa mutane da suke da mutunci da sanin ya-kamata da kima da mutunta jama’a. Ya ce kuma Karamar Hukumace da take da dimbin masu ilimin addini da ilimin zamani a fannoni daban-daban da suka hada da Farofesoshi da yawa da Daktoci da manyan ma’aikatan Gwamnati a manyan bangarorin.aikin.
A karshe, Alhaji Sani Mukaddas ya jaddada kira ga al’ummar Bichi su ci gaba da rike kambunsu na hadin-kai da zaman lafiya da tafiya a matsayin ‘yan uwan juna da suke a koyauahe idan ana maganar ci gaban Bichi.