Nadal Ya Lashe Kofin Gasar Tennis Na Us Open Karo Na 3

Refeal Nadal dan kasar Spain ya lashe kofin gasar kwallon tennis ta US Open, da aka kammala a birnin New York na Amurka, a wasan karshe da suka fafata da Kebin Anderson mai wakiltar kasar Afrika ta Kudu.

Nadal ya lallasa Anderson da kwallayen 6-3, 6-3, da kuma 6-4. Kuma karo na uku kenan da Nadal ke lashe kofin gasar US Open.

Wannan nasara ta bai wa Nadal damar lashe kofunan gasar ta Grand Slam daban daban har biyu a jere cikin wannan shekara daya, domin kuwa hi ne ya lashe kofin gasar French Open da ta gudana a watan Yuli.

Gasar kwallon tennis da ake kira Grand Slam dai ta kasu kashi hudu, wato US Open, French Open, Australian Open da kuma Wimbledon.

Zuwa yanzu Rafeal Nadal ke a matsayi na biyu wajen lashe Kofunan gasar kwallon Tennis din ta Grand Slam, inda ya ke da kofuna 16, yayinda Rodger Federer na Swizaland ke kan gaba da kofuna 19.

Pete Sampras na Amurka a matsayi na 3 da kofunan Grand Slam din 14, sai kuma Nobak Djokobic na kasar Serbia mai rike da kofunan gasar har guda 12.

Exit mobile version