Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta yi amai ta lashe kan alkawarin da ta yi na cewa maniyyata ba za su biya karin kudi ba kan karin dala 250 da aka yi na jigilar jiragen sama.
An bayyana cewa, kamfanonin jiragen sama na cikin gida da ke gudanar da aikin Hajji sun bukaci a kara kudin aikin Hajji da dala 250, sakamakon rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan, wanda zai bukaci karin lokacin zuwa kasar Saudiyya.
- Buhari Zai Kaddamar Da Ayyuka 7 A Ranar Talata –Fadar Shugaban Kasa
- An Ci Tarar Kamfanin Facebook $1.3 Biliyan
An rufe sararin samaniyar Sudan tun bayan barkewar rikici a watan Afrilu.
Sai dai da yake jawabi a Abuja yayin wani atisayen da aka shirya wa ma’aikatan NAHCON da hukumar alhazai ta jiha da masu gudanar da yawon bude ido masu zaman kansu, Zikrullah Hassan shugaban hukumar NAHCON ya bada tabbacin cewa ba za a bukaci maniyyatan su biya karin kudin ba.
“Kamfanonin jiragenmu na cikin gida bayan tattaunawa da dama sun amince da dala $250 a matsayin karin kudin tikitin jirgi domin gudanar da aikin na bana. Har yanzu muna neman duk hanyoyin da za mu warware wannan tsaiko. Har yanzu muna ba da gudummawa sosai don ganin an gaggauta warware rikicin Sudan ta yadda sararin samaniya zai ya bude kuma a daina kashe-kashen da ake yi wa al’ummar Sudan.”
“A NAHCON, muna neman dukkan hanyoyin da za mu tabbatar mun warware matsalar wannan karin kudin. Mun yanke shawarar cewa, ba za a bukaci maniyyata su biya karin kudade a hannun hukumomin alhazai na jiharsu ba. Ba za su bukaci karin kudi ba, ”in ji shi.
Sai dai a wata sanarwa a ranar Litinin, mataimakin daraktan yada labarai na NAHCON, Moisa Ubandawaki, ya ce hukumar ta yanke shawarar cewa maniyyatan za su biya kashi 40 cikin 100 na karin kudin jirgi bayan gwamnatin tarayya ta tallafa wa kamfanonin jiragen sama don yin jigilarsu.
“Hakan zai kara rage tsadar kudin jigilar maniyyatan Nijeriya. A baya dai gwamnati ta yi watsi da kashi 65% na kudin jiragen sama domin rage farashin aikin Hajji. Tare da wannan ci gaban, Karin dala 250 da aka tattauna da kamfanonin jiragen sama za a rage dala 55, ”in ji sanarwar.
“An kiyasta kowane mahajjaci zai biya dala 117, Hukumar ta yanke shawarar rage alawus na alhazai na 2023.”