Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

NAPTIP Za Ta Yi Amfani Da Bokaye Don Hana Safarar Mutane

by
4 years ago
in RAHOTANNI
2 min read
NAPTIP Za Ta Yi Amfani Da Bokaye Don Hana Safarar Mutane
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Hukumar NAPTIP ta bayyana cewa, a halin yanzu ta shirya daukan bokaye domin taimaka mata samun hujjojin hukunta shari’un safarar mutane da take dasu a fadin tarayyar kasar nan.

Jami’in watsa labaran hukumar Mista Josiah Emerole,ne ya sanar da haka a Abuja, in da ya ce lallai NAPTIP zata dauki Boakye aiki a matsayin jakadun yaki da safarar mutane a fadin kasar nan.

Idan za a iya tunawa shugabar Hukumar Julie Okah-Donli, ta fara bayyana haka a wani taron karawa juna sani daya  gudana a Abuja cewa, sun riga sun dauki bokaye a garin Benin da Edo a matsayin jakadu domin yaki da safarar mutane a kasar nan.

Labarai Masu Nasaba

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

Fashewar Gas A Kano: Ministar Jinkai Ta Nemi A Dauki Matakan Riga-kafi

“Abin da shugabanmu ta ce a ranar Litini shi ne a kokarin Hukumar na karfafa shari’un da take dasu na masu safarar mutane a fadin tarayyar kasar nan mun shirya jawo dukkan bangarorin alumma domin su fahinci gudummawar da zasu iya bayar wa a yakin da ake yin a kawar da safarar mutane”

“Mun lura da cewa amfani da tsafi da kalaman ranstuwa na daya daga cikin abubuwan da masu safarar mutanen ke amfani dasu wajen mallakar wadanda suka yi safararsu ta yadda ba zasu iya sanar da halin da suke ciki ba, abin da ke bamu matsala wajen samun hujojjin hukunta masu safarar mutane” in ji shi. Ya kara da cewa, Hukumar NAPTIP ta samu zuwa wani gawurtaccen wajen tsafi da ake kira Ayelala Shrines an jihar Edo in da anan ne ake tilastawa wadanda za a yi safarar yin ratsuwar ba zasu tona asirin masu safarar su ba.

Ya ce, an yi kokarin fahintar da bokayen halin da wadanda suka yi wannan rantsuwar ke shiga da yawa daga cikinsu sun fahinta kuma sun yi alkawarin ba zasu kara hurda da masu safarar ba har kuma sun yi alkawarin taimakawa domin cafko masu safarar mutane domin hukunta su.

Ya kara dacewa, lamarin rantsuwa a wurin bokaye ya dade yana ci ma NAPTIP tuwo a kwarya a tsawon shekaru, musamman shaidun da wadanda suka samu kan su a hannun masu safara mutane ke bayarwa na imanin da suka yi cewa rantsuwar da ake yi na matsafan na iya cutar dasu in sun ki bayar da hadin kai ko sun bayar da shaida akansu yayin da ake shari’a.

“Saboda haka muka ga bukatar amfani da wannan tsarin domin karfafawa wadanda suka shiga hannun masu safara zuciya domin su bayar da shaida, abin da in bamu samu ba NAPTIP ba zata iya hukunta masu safarar ba a gaban kotu”

“Hukumar mu a baya ta kama kuma ta kai ga hukunta matsafan a bisa hannunsu a safara mutane abin da yasa ba za a iya daukan su aiki kai tsaye a matsayin ma’aikatan Hukuman ba, sai dai zamu ci gaba da fadakar dasu a matsayin riga kafi ya fi magani”.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Bukatar A Dakile Matsalar Wutar Lantarki

Next Post

SHAFIN FARKO

Labarai Masu Nasaba

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

by Ahmed Muhammad Dan'asabe
3 days ago
0

...

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

Fashewar Gas A Kano: Ministar Jinkai Ta Nemi A Dauki Matakan Riga-kafi

by
3 days ago
0

...

Baki Biyu Bai Dace Da Matsayin Amurka Ba

Baki Biyu Bai Dace Da Matsayin Amurka Ba

by CMG Hausa
3 days ago
0

...

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

by
5 days ago
0

...

Next Post

SHAFIN FARKO

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: