A faninin kiwon Talo-talo a Nijeriya, ana matukar samun dimbin riba, har ila yau kuma fanni ne wanda ya ke daidai da sauran fannin kiwon sauran dabbobi, indai har an fara yin sa yadda ya dace.
Kafin gwamnatin tarayya ta haramta shigo da namansa cikin kasar nan, ana yawan shigo da naman nasa cikin Nijeriya kusan a kullum, inda hakan ya jawo raguwar sayen wanda ake da shi a cikin wannan kasa.
- Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba
- Dokar Hana Sayar Da Burodi Mara Shaida, Litar Mai Fiye Da 50 Ta Tabbata A Zamfara, Gwamna Dauda Ya Sa Hannu
Shin Kwana Nawa Talo-Talo Yake Kaiwa Kafin Ya Girma?
Talo-talo na kai wa tsawon sati talatin kafin ya girma, sannan yana yin akalla Kwai daga tamanin zuwa dari tare da fara kyankyashe su a cikin kimanin kwana ashrin da takwas, nauyin mata a cikin sati ashirin na kai wa; 4.5 zuwa 5, nauyin maza kuma yana kai wa daga 7 zuwa 8.
Tanadar Kayan Kiwonsa:
Ya kamata a samu kwararru a fannin, wadanda za su gina gurin da za a fara kiwonsu tare da sama musu wajen da za su rika samun wadatacciyar iska, sannan ya kamata kayan da za a yi amfani wajen gina musu dakin kwanan ya kasance ya dace da canjin yanayi, har ila yau kuma tare da samar musu abinci da kayan shan ruwa.
Tanadar Musu Da Abinci:
Ko shakka babu, Talo-talo na da mutukar cin abinci; wannan dalili ne yasa, wajibi ne wanda zai fara kiwonsu ya tabbatar da ya tanadar musu da abinci mai yawan gaske, domin idan suna samun abinci akai-akai suna yin saurin girma, haka nan ana son mai yin wannan kiwo nasu; ya rika sama musu abincin da ke dauke da sinadarin da ke gina musu jiki, musamman domin su kara samun kuzari tare da samar da Kwai mai tarin yawa.
Samun Ilimin Kiwon Talo-talo:
Yana da matukar kyau a tuntubi kwararrun da ke wannan fanni, domin samun ilimi a kan wannan kiwo na Talo-talo ko kuma a gudanar da bincike a cikin fannin, musamman domin kaucewa yin kuskure, musamman idan za a yi kiwon don kasuwanci.
Amfanin Kiwon Talo-talo Da Kuma Hadarin Da Yake Fuskanta:
Babu shakka, kiwonsa na da matukar alfanu, musamman ganin yadda ake samun dimbin riba tare da samun wadataccen nama. Kazalika, hanya ce da ke samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa tare da kara habaka tattalin arzikin kasar baki-daya.
Akwai kuma wasu kwari da suke iya yi musu illa, musamman a lokacin da suke kanana, saboda haka; ana so mai kiwon nasu ya tabbatar yana ba su irin kulawar da ta dace, har ila yau kuma; akwai kwayoyin cutar da za su iya harbin su, musamman a lokacin da suke kanana.
Bugu da kari, kiwon Talo-talo ba shi da wata whala, musamman idan aka samar da kayan da suka dace wajen kiwon nasu tare da samar da wajen da ya fi dacewa a kiwata su, haka nan ana samun kasuwanni da dama da ake sayar da su.
Shin Kamar Ribar Nawa Mai Kiwonsu Zai Iya Samu?
Ya danganta da yadda girmansu yake, domin babbar mace daya ta Talo-talo a Nijeriya, za a iya sayar da ita kan farashin daga Naira 17,000 zuwa 18,000.
Haka nan, macen Talo-talo daya na iya kyankyashe Kwai daga 10 zuwa 15; matukar suna samun kulawar da ta dace.