NAZARI: Kwamitin Binciken Naira Bilyan 58: Abin Da Ya Kamata Mutanen Jihar Katsina Su Yi

Daga El-Zaharadeen Umar

Tun lokacin zuwa wannan gwamnati ta APC a karkashin jagoranci Gwamna Aminu Bello Masari, ya yi wasu alkawura da daman gaske wanda kuma ya ce matsawar shi ne Gwamna da yardar Allah sai ya cika wannan alkawari da ya dauka.

Kwamitin binciken da Gwamna Aminu Bello Masari ya kafa, ba ya daga cikin alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe, sai dai bayan da ya ci karo da wasu bayanai da suke nuni da cewa wasu kudi sun yi layar zana a jihar Katsina, sai ya daukar wa kansa cewa zai bi yadda doka ta ce domin ganin wadannan kudade sun dawo.

Bai yi kasa a gwiwa ba, ya kafa kwamitin da zai yi wannan babban aiki. Domin kamar yadda ya sha fada, sun ga wasu abubuwa da suke ganin ba-daidai ba, a kundin daftarin mika mulki da gwamnatin da ta gabata ta ba su, saboda haka za su bi diddigin wannan batun domin dai kawai a hadu a  tashar gaskiya.

Kafa wannan kwamiti da Gwamna Aminu Bello Masari ya yi ya ba mafi yawancin mutanen jihar Katsina kwarin gwiwar cewa lallai wani abu ya faru wanda ba daidai ba, saboda haka ana bukatar gaskiya ta yi aikinta akan ko wane ne.

Bayan haka bayanan sirri sun tabbatar da cewa kafin kafa wannan kwamitin sai da gwamnatin da wasu mutane da ake gani da kima a wannan jiha suka yi iyakar kokarinsu domin a wanye lafiya da mutanen tsohuwar gwamnatin, amma haka ba ta samu ba.

Kazalika an sha ambato Gwamna Aminu Bello Masari yana bayanin cewa duk wanda ya san dukiyar jama’a na hannunsa, to ya biyo dare ya damkata a hannun gwamnati ba tare da wani ya sani ba, kuma ba wanda zai san an yi haka. Muna ganin wannan shi ne abu mafi girma da nuna alkunya da Gwamna Masari ya yi domin kawai a rabu lafiya da mutanen tsohuwar gwamnatin.

Ni a ganina ina da abubuwa da daman gaske da nake hangen ya kamata kowane dan jihar Katsina ya bada tasa gudumuwa wajen ganin wannan kudiri na dawo da wadannan makudan kudade sun dawo cikin aljihun gwamnatin jihar Katsina domin ci gaba da ayyukan da aka sa a gaba.

Kafa wannan kwamiti ke da wuya, wadanda aka dora wa alhakin tafiyar da wannan kwamiti suka bada dama ga kowane dan jihar Katsina idan yana da korafi ya gabatar da shi a gaban wannan kwamiti, sannan ya shirya zuwa kare wannan korafi nasa duk lokacin da bukutar hakan ta taso. Haka kuma aka yi, inda aka bada mako hudu a gabatar da korafe-korafe.

Abu na farko da ya fara zama matsala ko barazana da wasu suka yi kokarin haifarwa shi ne, yadda aka shirya wasu matasa suka yi dafifi a muhallin da wannan kwamitin zai rika zama domin kawo tarnaki ga wannan babban aiki, ta hanyar yin zanga-zagan, wanda kana ganin haka ka san da walakin, goro cikin miya, ma’ana dai wadanda suke cikin wannan badakala ne suka shirya hakan.

Wannan mataki bai taba zama abin kallo ko lura ba ga masu wannan aiki na kwamiti, saboda haka kwamitin ya ci gaba da aikinsa kamar yadda aka ba shi dama, cewa akwai wasu zarge-zarge na wasu kudade da aka dauke su dan-das, ma’ana babu wani abu da aka nuna an yi da wadannan kudade kuma babu wani bayani gamsasshe.

Wani abin burgewa game da wannan kwamitin, a tarihin irin wadannan bincike-bincike za a ga ana binciken yin kwangila da sayan wasu abubuwa da ake ganin an yi kuriciyar bera wajen aiwatar da su, amma Gwamna Aminu Bello Masari ya ce, wannan ba ya daga cikin manufofi na kafa wannan kwamitin, abin da kawai yake so shi ne wadannan kudade da ake dauki dan-das, suna ina? Me aka yi da su? A ba kowa dama ya zo ya wanke kansa.

Sakamakon yadda kowa ya sani yanzu babbar matsalar da ake fama da ita a wannan kasa ta mu, ita ce bangaren Shari’a ya yi matukar baci ta bangaren kawo cikas da tarnaki akan wani batu da ya kamata su bangaren Shari’ar su bada tasu gudumuwa domin ganin an yi nasara, to amma akasin haka ake samu.

Lauyoyin wadanda ake zargi sun shirya tsaf domin kare wadanda ake zargi kamar yadda dokar kasa ta bada, wanda su kuma Lauyoyin suka yi amfani da wannan damar wajen kawo cikas na ganin wannan aiki ba a yi shi yadda ya kamata ba, amma an ce shure-shure ba ya hana mutuwa, a karshe dai haka ta kusa cimma ruwa.

Ina daga cikin wadanda suke bibiyar zaman wannan kwamiti tun daga lokacin kafa shi har zuwa ranar da ya yi zamansa na karshe da kuma mika rahotan wucin gadi da kwamitin ya mika wa Gwamna Aminu Bello Masari, duk a gaban idona saboda haka abubuwa da yawan gaske na sani game da wannan kwamiti.

Kamar yadda na fada, wannan kwamitin ya sha wuyar gaske a hannun Lauyoyin wadanda ake zargi, inda har ta kai kotun daukaka kara da ke Kaduna ta dakatar da zaman wannan kwamitin har sai ta kammala sauraron karar da aka shigar a gabanta, inda Lauyoyin da wadanda ake zargi suka ce ba su da natsuwa da shugaban Kwamitin, Mai Shari’a Muhammad Suraj, a karshe dai kotun ta bada umarnin a cire shi a matsayin shugaban kwamitin a maye gurbinsa da wani.

Wannan mataki shi ya baiwa Gwamna Aminu Bello Masari damar nada Mai Shari’a Ado Ma’aji domin ya kammala wannan aiki da ya shafe fiya da watanni goma sha biyar ana yinsa. Sai dai kuma wannan fa bai yi wa wasu dadi ba, musamman Lauyoyi da kuma wadanda ake zarge, su sun so a ce an maida hannun agogo baya, ma’ana a sake shirya sabon zaman wannan kwamiti domin su hana ruwa gudu.

Sannan wani abu da mutanen jihar Katsina ba za su taba mantawa da shi ba, shi ne duk duniya ta shaida yadda wasu mutane biyu da suke da alaka da tsohon Gwamna Ibrahim Shehu Shema suka bayyana akan wannan kwamiti, inda suka bayyana yadda aka yi watanda da dukiyar jama’a, wanda ina ganin wannan kadai ya isa babbar shaida a gaban Alkali.

Malam Nasiru Ingawa ya bayyana a gaban wannan kwamitin, inda ya fadi yadda suka tarwatsa wasu kudade da ke karwashin ofishinsa na SURE-P, sai dai kuma ‘yan uwansa ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP suna cewa wannan magana ba su da alaka da ita, amma ba su ce karya yake ba.

Bayan haka, baban Dogarin Tsohon Gwamna, Shehu Muhammad Koko ya bayyana a gaban wannan kwamitin bayan da farko ya ki amsa gayyatar kwamitin, amma da ya ga fadan ya fi karfinsa ya zo ya bayyana yadda ya yi da zunzurutun kudi har Naira Miliyan 680 a cikin kwanaki biyu kacal daf da fara zaben shekarar 2015, wannan ba wanda ya ce karya yake yi, har ma ya taimaka wa wannan kwamiti da wasu takardu a matsayin shaidar abin da ya aikata.

Shi ma da yake jawabi ga manema labarai, Mukadashin Shugaban kwamitin, Mai Shari’a Ado Ma’aji ya bayyana cewa daga cikin takardun da aka gabatar a gaban kwamitin akwai wasu da ba su dace da yanayin aikinsu ba, shi ya sa suka ajiye su a gefe guda.

Wani abin ban sha’awa da kuma burgewa game da kokarin Gwamna Aminu Bello Masari game da wannan kwamitin shi ne, irin yadda ya rufe ido wajen gudanar da wannan aiki ba tare da lura da cewa shi yanzu yana kan karagar mulki ba, kuma za a wayi gari ya gama nasa.

Sai dai ya sha nanata cewa wannan kwamitin ko ba komai, kafa shi wata alama ce ta yi wa kai iyaka, domin kuwa su ma duk ranar da suka kammala nasu aikin ba za su ji tsoron abin da zai biyo baya ba, saboda yadda suka yi wa tufkar hanci.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin matakin Shari’a da wannan gwamnati za ta bi domin ganin an dawo da wadannan makudan kudaden da Gwamna Masari ya ce, idan aka dawo da su, za su canza rayuwar mutanen Katsina ta fuskoki da dama.

Sannan ga masu adawa da wannan muhimmin aiki shi ne kullin abin da suke cewa wai bai kamata a ce kwamitin ya gama aikinsa da wuri ba, sannan ya mika rahoto, sai dai har yanzu ba su kawo wata doka da ta ce kada a yi hakan ba.

Ni a ganina kamata ya yi duk dan jihar Katsina kowa ya bada ta sa gudumuwar domin wannan jan aiki ya samu nasarar da ake bukuta na ganin Gwamna Masari ya yi nasarar dawo da wadannan kudade cikin baitul-malin gwamnatin jihar Katsina, ta inda su ma za su sa na mujiya wajen ganin irin ayyukan da za a yi da su.

Samun nasarar wannan aiki, nasarar mutanen Katsina ce baki daya. Saboda haka da ni da kai, da ku, da su kowa ma, ya kamata ya yi wani abu na zahiri da badini domin haka ta cimma ruwa. Sannan duk abubuwan da suka faru ya zamo wa’azi da gargadi ga ‘yan baya, saboda an ce da na gaba ake gane zurfin ruwa.

 

El-Zaharadeen Umar ya rubuto mana ne daga Katsina

 

Exit mobile version