A lokacin zafi na bana, yayin tafiye-tafiyen da suka shafi guje wa zafi da rangadi da sayayya da na abubuwan al’adu, ziyartar kasar Sin da ake wa lakabi da China Travel, na kara samun masoya a fadin duniya. Sakamakon nazarin da CGTN ta gudanar ta kafar intanet, ya nuna kaso 92.9 na masu bayar da amsa na ganin batun na China Travel, na nuna karuwar sha’awar kasa da kasa kan kasar Sin.
A cewar hukumar kula da shige da fice ta kasar Sin, an samu tafiye tafiyen baki zuwa kasar Sin har miliyan 22.914 a rabin farko na bana, adadin da ya karu da kaso 20.4 a mizanin shekara shekara, inda ya ci gaba da samun kuzari.
Cikin nazarin, kaso 92.8 na masu bayar da amsa sun ce yawan shirye-shiryen da aka wallafa a kafofin sada zumunta game da ziyara a kasar Sin na ci gaba da kara musu sha’awar sanin kasar da ziyartar ta.
Kaso 87 kuma sun yi imanin zuwa kasar Sin da kansu zai taimaka musu kara samun cikakkiyar fahimta game da kasar da ainihin al’adun da al’ummun da yanayin ci gabanta.
An wallafa nazarin ne a dandamalin CGTN na harsunan Turanci da Sipaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda cikin sa’o’i 24 mutane 7,085 masu amfani da intanet suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














