Abdulazeez Kabir Muhammad" />

NDLEA Ta Gurfanar Da Mutum Biyu Da Ta Kama Da Kilogiram 2,139 Na Wiwi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) a ranar Juma’a ta tura mutum biyu zuwa Kotun Koli ta tarayya dake Lagos, saboda zargin su da safarar kilo 2,139 na “Cannabis Sativa” wanda aka fi sani da tabar wiwi, a na tuhumar Alex Adibeli mai shekaru 43, da kuma Michael Ifeakachu, mai shekaru 46 da aikata laifuka biyu na fataucin miyagun kwawoyi.

Mista Irmiya Aerna, jami’in NDLEA, a cikin tuhumar da ake musu, ya bayyana cewa wadanda ake zargi sun aikata laifin ranar 3 ga Mayu a Legas.

Aerna ya ce sun yi niyyar safarar kilogiram 2,139 na wiwi, wanda aka boye a cikin babbar Motar MAN don gudun kar a gano su.

Wannan laifin, ya ce, ya saba wa sashe na 11 (b) da kuma 14 (b) na dokar hukumar NDLEA Dokar N 30 na 2004.

Wadanda aka tuhuma sunyi ikirarin cewa ba su aikata laifin da ake zargin su ba. Bayan an amshi rokon da wadanda ake tuhuma suka yi, Lauya mai kare su, Benin Benson Ndakara, ya yi kira ga kotu da ta bada beli wadanda yakw karewa, mai shari’a Saliu Saidu ya amince da wanda ake tuhumar su biya belin Naira miliyan 10 da biyu tare da mutum biyu da zasu tsaya musu.

 

Saidu ya ba da umurni cewa wajibi ne wadanda zasu tsaya musu su kasance sun mallaki kadara adadin kudin belin nasu kuma dole su gabatar wa da kotu takardun kadarar don tantancewa. Kotu ta kuma yin umurni na biyu cewa, dole ne ya zama ma’aikacin gwamnati na Tarayya ko na jiha.

Alkalin ya dage sauraran karar zuwa ranar 24 ga watan Oktoba

Exit mobile version