Gwamnatin tarayya tare da kamfanin sarrafa takin zamani ‘Fundação Getulio Bargas’ na Kasar Brazil, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sarrafa takin zamani da samar da ingantacen Iri da kuma kudade ga fannin aikin noma a Nijeriya.
Sun sanya hanun ta hanyar ma’aikatar samar da wadataccen abinci na wannan kasa.
- Halartar Shugaba Xi Taron APEC Da G20, Da Ziyarar Aiki A Peru Da Brazil Sun Kasance Wata Hanyar Sada Zumunta Da Hadin Gwiwa
- An Yi Wa Shugaban Ƙasar Brazil Lula Da Silva Tiyatar Ƙwaƙwalwa
Hakan na kunshen ne cikin sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar, wacce Daraktan Yada Labarai da Hurda da Jama’a; Abiodun Oladunjoye ya fitar a Abuja.
Sanarwar ta bayyana cewa, Babban Sakataren Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wataceccen Abinci, Farfesa Carlos Iban Simonsen ne ya rabbata hannun a madadin gwamnatin tarayya.
An rattaba hannun ne, a Birnin Rio de Janeiro na kasar ta Brazil a bayan fagen taron shugabanin kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki a duniya.
Kazalika, sanarwar ta sanar da cewa; rattaba hannun ya bode wani sabon fage a tsakanin Nijeriya da aikin da ake yi na amfani da fasahar zamani, don kara bunkasa fannin aikin noma a fadin wannan kasa.
A cewar sanarwar, aikin wanda aka faro tun a shekarar 2018, zai lashe kimanin dala biliyan 1.2, wanda kuma da ma hadaka ce tsakanin Nijeriya da kasar ta Brazil.
Haka zalika, an tsara aikin ne don kara habaka fannin aikin noma na kasar nan, ta hanyar yin amfani da kwararrun da suka fito daga Kasar Brazil.
Har wa yau, sanarwar ta sanar da cewa; bankin Deutsche na inganata aikin noma ta hanyar amfani da fasahar zamani da kuma yada ilimin aikin noman nan da zuwa shekaru goma masu zuwa.
Nan da shekaru biyar masu zuwa, aikin zai gano tare kuma da tallafawa aikin noma a kananan hukumomi 774 tare da bai wa manoman tallafin kudi, domin kara habaka fannin aikin noma da tattalin arziki.
Fashedemi ya sanar da cewa, wannan hadaka; za ta bai wa Kasar Brazil damar jawo Nijeriya a jiki, musamman don gaggauta bunkasa fannin aikin noma a kasar.
A cewar tasa, ta hanyar haka ne za mu samu damar fito da albarkar da ke fannin zuba hannun jari a manyan ayyuka, musamman don samar da wadataccen abinci.
A karkashin yarjejeniyar, masu zaman kansu a fannin sarrafa takin zamani da samar da ingantaccen Iri, ana sa ran za su samu kudaden shiga kimanin dala biliyan 4.3.