Daga Abubakar Abba,
An bayyana cewa Kasashen Sudan da Chadi da kuma Nijeriya ne suka fi fitar da Karo zuwa kasuwannin duniya.
Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da sashen Kasuwanci Da Samar Da Ci Gaba (UNCTAD) na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, inda rahoton ya bayyana Sudan, wacce keda kashi 66 a cikin dari na jimlar wanda take fitar wa.
A cewar rahoton, kasar Chadi na da kashi 13 a cikin dari, sai kuma Nijeriya na da kashi 8.5 a cikin dari daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2016.
Rahoton ya ci gaba da cewa, a shekarar 2000, Nijeriya da kasashen Senegal Sudan, sun noma Karo mai babbar darajar da da na’urorinsu na cikin gida na sarrafa Karo.
Sai ingantacce Karo, rashin tsara yadda za samar masa da kasuwarsa, rabar dashi saboda ayyukan ‘yan taddar Boko Haram, musamman wajen samar dashi mai yawa wga masana’antun dake yin amfani dashi wajen hada magunguna.
Rahoton ya bayyana cewa, Nijeriya za ta iya samun dimbin kudaden shiga daga kara fadada Noman Karo da kuma fitar dashi zuwa kasuwannin duniya.
A cewar rahoton ta hanyar samar da kyawawan dabaru kara samar dashi a cikin kasar, iya ya kara da cewa, gwamnati dole ne ta fito da hanyoyin kara samar wa da kanta kudaden shiga ta hanyar fitar da amfnin gon zuwa kasuwannin duniya.
Ya ce, akwai matukar bukatar Nijeriya ta yi amfanin da yanayin da ake a ciki a yanzu, wajen kara habaka fannin aikin noma a kasar nan.
Bugu da kari, a kwanan baya ana ruwaito Shugaban kungiyar (FACAN) Dakata Victor Iyama ya bayyana cewa Nijeriya za ta iya samun dimbin kudaden shiga daga kara fadada Noman Karo da kuma fitar dashi zuwa kasuwannin duniya.
“ Tabbas Nijeriya za ta iya samun dimbin kudaden shiga daga kara fadada Noman Karo da kuma fitar dashi zuwa kasuwannin duniya”.
A cewar Shugaban kungiyar Dakata Bictor Iyama, ta hanyar samar da kyawawan dabaru kara samar dashi a cikin kasar, Iyama ya kara da cewa, gwamnati dole ne ta fito da hanyoyin kara samar da kudaden shiga ta hanyar fitar da amfnin gon zuwa kasuwannin duniya.
Shugaban kungiyar Dakata Bictor Iyama ya bayyana cewa, akwai matukar bukatar Nijeriya ta yi amfanin da yanayin da ake a ciki a yanzu, ya kara da cewa, ya zama wajibi a kara habaka fannin aikin noma a kasar nan.
“Akwai matukar bukatar Nijeriya ta yi amfanin da yanayin da ake a ciki a yanzu, ya zama wajibi a kara haba fannin.