Abba Ibrahim Wada" />

Nijeriya Ta Gayyaci Afelokhai Bayan Uzoho Ya Ji Ciwo

Kociyan tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya Gernot Rohr ya gayyaci mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International, Theophilus Afelokhai domin ya maye gurbin mai tsaron raga Francis Uzoho wanda ya ji rauni.
A ranar Litinin ne kungiyar kwallon kafa ta Cardiz dake buga wasanni a kasar Sipaniya ta bayyana cewa mai tsaron ragar wanda yake buga mata wasa ya karye a kirjinsa kuma zaiyi jinyar makonni hudu hakan yasa Nijeriya ta canja shi.
Nijeriya dai ta gayyaci Francis Uzoho ne domin ya buga wasannin da kasar za ta buga da kasashen Afirka ta kudu a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka da kuma wasan da kasar za ta fafata da kasar Uganda na sada zumunci.
Afelokhai, wanda tsohon dan wasan Kano Pillras ne zai shiga cikin tawagar ‘yan wasan na Super Eagles ne tare da takwaransa na kungiyar Enyimba, Ikechukwu Ezenwa, wanda duka tare suke buga wasa a kungiya daya.
Afelokhai dai yayi kokari sosai a wasannin cin kofin nahiyar Afirka da kungiyar Enyimba ta wakilci Nijeriya kuma ya taba zuwa wasan kusa dana karshe da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a shekara ta 2009.
A ranar 17 ga wannan watan ne Nijeriya za ta buga wasa da kasar Afirka ta kudu kuma idan ta samu nasara a wasan ta samu tikitin zuwa kasar Kamaru domin buga kofin nahiyar Afirka sannan kuma bayan kwana uku ta buga wasa da kasar Uganda a wasan sada zumunta a nan Nijeriya.

Exit mobile version