Rabiu Ali Indabawa" />

Nijeriya Ta Tafka Asarar Naira Tiriliyon 2.27 A Kasuwa

Masana na ganin cewa, Nijeriya za ta shiga cikin matsin tattalin arziki sakamakon cutar Coronabirus, wanda ta sanadiyyar cutar Nijeriya ta tafka asarar Naira tiriliyon 2.27 a cikin kasuwancinta wanda ya kai ga an samu karuwar marasa aikin yi a cikin kasar. Wani kamfani mai suna Berraki Partners ne ya bayyana hakan.

Kamfanin ya ce, “cutar COBID-19 ta durkushe harkokin kasuwanci a duniya musammam ma a Nijeriya. Sakamakon wannan cuta ta COBID-19 wanda ta janyo karyewar tattalin arziki a duniya gabaki daya a wannan shekara ta 2020, inda aka kiyarta cewa an tafka asarar dala tiriliyon 2.7.”

A cewar kamfanin, za a sami karuwar marasa aikin yi musammam ma wadanda suke aiki a kamfanoni sakamakon koma baya da kamfanoni za su samu.

Kamfanin Berraki Partners ya bayyana cewa, da wannan tsala da duniya ta samu, shugabannin ‘yan kasuwa su tabbatar da cewa za su sami gagarumar canji a bangaren kasuwancinsu.

Ya kamata shugannin kasuwanci su samar da hanyoyin wanda za su bi wajen farfadowa daga wannan lamari, domin karfafawa harkokin kasuwancinsu a nan gaba. Ta kara da cewa, wannan cuta ta Coronabirus ta girgiza tattalin arzikin dukiya gaba daya.

Ta ce, a shekarar 2019 aka bai wannan cuta ta Coronabirus suna COBID-19, inda aka sami sama da mutum 600,000 suna dauke da wannan cuta, yayin da cutar da kashe mutum 30,000 a duniya baki daya a ranar 28 ga watan Maris.

Lokacin da kasa take kokarin samun mafita daga wannan hatsari, rahoton ya bayyana cewa, Nijeriya ta afka cikin matsanancin tattalin arziki sakamakon wannan cuta ta COBID-19. Musamman ma manyen kasashe guda hudu abokanan kasuwancin Nijeriya wadanda suka hada da kasashe irin su China da Amerika da Spain da kuma Netherlands, wanda aka kiyasta cewa Nijeriya tana shigowa da kayayyaki wadanda suka kai kashe 45 daga wadannan kasashe, inda yanzu komai ya tsaya cik, sakamakon dokar hana zirga-zirka domin kar cutar COBID-19 ta yadu.

A cewarta, idan lamarin ya ci gaba da shafar harkokin kasuwanci har zuwa wata biyu masu zuwa, to Nijeriya za ta tafka asarar naira tiriliyon 2.23 daga wadannan kasashe guda biyar da take shigowa da kayayyaki daga can, wanda hakan zai haifar da karancin kayayyakin bukatuwa.

Daga kasashe guda biyar da Nijeriya ta ke fitar da kayayyakinta, an kiyaesa cewa, Nijeriya ta tafka asarar naira tiliyon 2.27 na kayayyakin da take fitarwa a sasuwannin duniya, sakamakon rufe iyakokin kasa da kasa da bayar da tazara da dokar hana fita a sauran kasashen duniya da kuma kasar Nijeriya.”

Berraki Partners ta ci gaba da cewa, kasuwannin hannun jari ya durkushe kamar yadda masana suka ayyana sakamakon wannan cuta, an dai samu matsala a kan kudaden haraji da raguwar ribar da ake samu da karyewar darajan kayayyakin bukatuwa wanda mutane suke fuskanta da kuma yadda kamfanoni ba sa iya fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen ketare, wanda ya sa kamfanonin za su rage yawan ma’aikatan da suke da su.

Bugu da kari, ta bayyana cewa, lamarin zai fi kazanta ne idan aka rage darajar naira a kasuwan duniya, kamar yadda babban bankin Nijeriya yana shirin yage darajar naira wanda ya ware dala biliyon 30 don gudanar da lamarin.

A cewarta, kashe 19.83 ta sauka daga dala biliyan 45.175 a wayan Yunin shekarar 2019, inda take dala biliyan 36.221 a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2020 na farashin mai a kasuwan duniya.

Babban bankin Nijeriya ta dai-daita tsakanin naira da dala wanda dala daya take naira 360 a kasuwancin banki, inda da take naira 306 ta yi tashin kwakron zabi zuwa 380 a kan kowacce dala daya, yayin da ta dawo naira 365.

Rahotan ya bayyana cewa, an sami karancin jama’ar da ke sayan dalar. Da wannan ne rahoton ya bayyana cewa, kashi 21 na mutane mutanen Nijeriya miliyan 99.6 suke tanadin kudi. A wannan lokaci san sami sama da mutane miliyan 78 wadanda ba sa yin tanadi.

A cewarta, mafiyawancin wadannan mutane sana jiran albashin su ne idan wata ya kare, yayin da wadanda suke samun kudaden a duk kullun suke boye kudadensu a cikin gidajensu.

Mafi yawancinsu sun fi bukatar su sayi kayayyakin bukatuwansu na yau da kullum su ijiye su, inda za su ci gaba da amfani da wadannan kayayyaki har ha tsawan lokacin da za su kare.

Exit mobile version