Gwamnatin Tarayyar ta yaba wa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas, wanda ya haifar da sakin wasu Isra’ilawa uku da kuma sakin Falasɗinawa daga gidajen yari na Isra’ila. Yarjejeniyar ta kuma bayar da damar kai kayan agaji da taimako ga yankin Gaza.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta fitar a Abuja, an bayyana jinjina ga ƙasashen Masar, da Qatar da Amurka bisa ƙoƙarin da suka yi wajen cimma wannan yarjejeniya. Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da nasarar aiwatar da mataki na biyu da na uku na wannan shiri tare da tabbatar da warware rikicin Falasɗinawa da Isra’ila ta hanyar samar da “ƙasashe biyu.”
- Gaza: Ana Gudanar Da Kirismeti Lami A Bethlehem Mahaifar Yesu Almasihu
- Ko Me Ya Sa Amurka Ta Gaza Cimma Burinta Na Yakin Kimiyya Da Fasaha Da Kasar Sin?
An saki Isra’ilawa uku mata da aka yi garkuwa da su tsawon watanni 15 a madadin sakin Falisɗinawa 95 da ke gidajen yarin Isra’ila. Wannan yarjejeniya mai matakai uku na da nufin kawo ƙarshen rikicin Gaza, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane daga 2023 zuwa yanzu.