• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Za Ta Haɗa Gwiwa Da Amurka Wajen Inganta ‘Yancin ‘Yan Jarida

by Sulaiman
1 year ago
Amurka

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana ƙudirin ma’aikatar sa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin ƙasar Amurka domin inganta ‘yancin manema labarai a Nijeriya.

Rabi’u Ibrahim, mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, ya bayyana hakam a takardar da ya rattaba wa hannu cewa, Idris ya faɗi hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wani zama da Jakadan Amurka a Nijeriya, Mista Richard Mills, a ofishin sa da ke Abuja a ranar Laraba.

  • Gwamnati Za Ta Gina Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa Sabbin Gidaje A Kano
  • Dakta Gadan-ƙaya Ya Bada Haƙuri Kan Zargin Auren Jinsi Da Ya Yi A Bauchi

Ministan ya ce: “Jakadan ya yi magana kan waɗansu abubuwa da yake ganin ya dace mu kula da su don inganta ‘yancin ‘yan jarida, mu kuma mun ba shi tabbaci kan irin abubuwan da muke yi, kuma ya ce, ya san cewa muna yin abin da ya dace wajen tabbatar da cewa, aikin jarida a Nijeriya ba kurum yana da cikakken ‘yanci ba ne, a’a har ma za a iya cewa yana daga cikin waɗanda suka fi ko’ina samun ‘yanci a faɗin duniya.

“Na san cewa, akwai wasu ‘yan matsaloli nan da can, kuma muna aiki don kulawa da irin waɗannan wuraren don dukkan mu mu ci moriyar abin da ake kira ‘yancin aikin jarida, wanda muhimmi ne a kowace ƙasa mai da’awar mulkin dimokuraɗiyya mai ƙarko.”

Ministan ya nanata yadda gwamnatin Tinubu ta ba ‘yancin ‘yan jarida muhimmanci kuma ya tabbatar da cewa, za ta ci gaba da inganta ‘yancin manema labarai a ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

Ya ce, sun kuma tattauna kan yadda za su haɗa kai su yi aiki tare wajen yaƙar baza labaran bogi da na ƙage a ƙasar.

Ya ce: “Ya yi magana kan labaran bogi da na ƙage da na ƙarya, duk waɗannan abubuwan mun tattauna kan su. Dukkan mu mun yi amanna da cewa babu yadda za a yi ka gina al’umma ingantacciya a yayin da kake yaɗa labaran ƙarya kuma ba ka ɗauki batun labaran bogi da na ƙage da gaske ba.”

A nasa jawabin, Jakada Mills ya ce zaman da suka yi da ministan sun yi shi ne domin su tattauna kan hanyoyin ƙarfafa dangantakar da ke akwai tsakanin gwamnatin Amurka da ma’aikatar, musamman abin da ya shafi ‘yancin ‘yan jarida da haƙƙoƙin manema labarai.

Ya yi la’akari da ƙoƙarin da ministan ke yi wajen haɓaka ‘yancin ‘yan jarida da haƙƙoƙin manema labarai a Nijeriya.

Jakaden na Amurka ya yi la’akari da babban ƙalubalen da matsalar baza labaran bogi ke janyowa, musamman ga ƙasashen da ke tafiyar da mulkin dimokiraɗiyya a faɗin duniya.

Ya ƙara da cewa sun kuma yi musayar ra’ayi da shawarwari kan yadda za a magance ƙalubalen.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma
Manyan Labarai

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP
Labarai

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu!
Rahotonni

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
Next Post
Gandiroba Ya Hallaka Abokin Aikinsa Kan Abinci A Bauchi

Gandiroba Ya Hallaka Abokin Aikinsa Kan Abinci A Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.