Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya kaddamar da asibiti wanda jami’an hukumar za su dinga amfani da shi yayin da suke bakin aiki a kan iyakar kasa na Gurin da ke cikin Jihar Adamawa.
Shugaban ya kaddamar da asibitin ne a yau Alhamis 11 ga watan Fabarairun 2021.
Babandede ya sauka garin Yola inda ya kai ziyara ta musamma ga Gwamnan Jihar Adamawa, Rt Hon. Ahmadu Umaru Fintiri a gidan gwamnati da ke gaarin Yola babbar birnin jiha.
Gwamman ya yaba wa shugaban hukumar ta NIS a bisa gudanar da aiki tukuru da samar da wajen aiki mai kyau ga jami’an hukumar.
Da yake jawabi, CGI Babandede ya yi matukar godiya ga gwamnan bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar da dabaru da kuma tallafa wa jami’anta da ke Jihar Adamawa, domin samar da tsaro a bakin iyakar jihar da kasar Kamaru.
Ya tabbatar wa gwamnan cewa sakamakon wannan aiki da aka kaddamar a Belel, jihar za ta samu gagarumin tsaro ta hanyar hukumar shige da ficen ta Nijeriya.
Bayanan hakan sun zo a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na NIS, DCI James Sunday ya rattaba wa hannu ya aike wa LEADERSHIP A Yau.