A kokarin da hukumar kula da shige da fice ta kasa NIS ke yi na shawo kan kalubalen jinkirin samar da fasfo ga dimbin masu bukata a jihar Kaduna, hukumar ta kaddamar da cibiyar samar da ingantaccen fasfo da za a iya nema ta yanar gizo a jihar.
A bikin kaddamar da cibiyar da aka gudanar a ranar 29 ga watan Agusta, 2023, gwamnan jihar Kaduna wanda shugaban ma’aikatansa kuma tsohon Kwanturolan NIS na jihar Kaduna, Alhaji Sani Kila, ya wakilta, ya bayyana matukar godiya ga hukumar NIS bisa kafa wannan katafariyar cibiya a jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa, Nijeriya na alfahari da Hukumar, kasancewarta ta farko a nahiyar Afirka kuma ta biyar a Duniya wajen rungumar tsarin gudanar da yin ingantaccen fasfo ta hanyar intanet. Don haka, Alhaji Sani Kila ya jaddada goyon bayan gwamnatin jihar Kaduna ga hukumar NIS.
A nata jawabin, Mukaddashiyar Shugabar Hukumar NIS, CGI Caroline Wura-Ola Adepoju, ta ce hukumar NIS ta dukufa wajen ganin ta samar da ingantaccen fasfo na intanet a duk fadin jihohin Nijeriya.
Mukaddashiyar CGI ta nanata cewa, dole sai an tanadi Nambar katin dan kasa (NIN) kafin a iya samun damar neman fasfo din ta intanet, kuma dole bayanan da za a bayar su yi dai-dai da wadanda ke cikin katin dan kasa. Matukar an cika sharadi kuma babu kalubalen kayan aiki, za a samu fasfo cikin sati biyu zuwa shida.