Abdulrazaq Yahuza Jere" />

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Jami’anta Na Iyakar Kasa A Efraya Ta Jihar Kuros Riba

Kaddamar Da Sansani

Shugaban NIS Muhammad Babandede (na uku daga hagu), Kwanturolan NIS na Jihar Kuros Riba Mista Okey Ezugwu (a hagu), Babban Sakataren Tsaro na Jihar Kuros Riba Dakta Alfred Mboto (na biyu a hagu) da sauran manyan baki yayin kaddamar da sansanin jami’an na NIS a Efraya ta Jihar Kuros Riba.

A ci gaba da kokarin da yake yi na karfafa ayyukan jami’ai a kan iyakokin kasa da bakin-haure ke amfani da su wajen silalowa cikin kasa, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya kaddamar da karin wani sansani na iyaka a yankin Efraya na Jihar Kuros Riba.

Ya kaddamar da sansanin ne a ranar Juma’ar nan 19 ga Fabarairun 2021.

Da yake jawabi a yayin kaddamarwar, Babandede ya bayyana cewa samar da sansanin wani karin tagomashi ne a kokarin da hukumar ke yi na tabbatar da cewa an gina sansanin jami’ai a dukkan iyakokin kasar nan domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare na kula da iyakoki kamar yadda ya kamata.

Ya ce a karkashinsa, hukumar ta ba da fifiko ga gina wadannan sansanonin ne domin shawo kan karancin ababen more rayuwa na aiki da ake bukata domin jami’ai su ji dadin gudanar da ayyukansu, inda ya nunar da cewa sansanonin sun bai wa NIS damar magance kalubalen da ake gamuwa da su wajen dakile aikata miyagun laifuka a iyakokin kasa irin su fashin daji da safarar bil’adama.

CGI Babandede ya kara da cewa kafa sansanonin jami’ai a iyakokin kasa ya karfafa tsaro a iyakokin tare da kara wa jami’ai himmar aiki saboda sun samu kyakkyawan muhalli na aiki. Ya ce sansanin da aka kaddamar a Efraya yana daga cikin wadanda ya kaddamar a kwanan nan kamar a Bele na Jihar Adamawa da na Adaha Offing a Jihar Akwa Ibom.

Babandede ya gode wa manyan bakin da suka halarci bikin kaddamarwar. Musamman ya jinjina wa Gwamnan Kuros Riba Sanata Ben Ayade da Basaraken Karamar Hukumar Etung, Ntue Atue, Dakta Emmanuel Oru Ojong da kuma shugaban karamar hukumar yankin.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’a na NIS, DCI Sunday James, ta ce shugaban hukumar ya sake nanata kudirinsa na ziyartar duk sassan da jami’ansa ke aiki domin share musu hayawayensu da kansa ba sako ba, domin nuna shugabanci nagari.

Exit mobile version