NIS Ta Kara Wa Kananan Jami’anta 1,899 Girman Mukami

Domin kara musu kwarin gwiwar ci gaba da kwazon aiki da jajircewa, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Muhammad Babandede ya amince a kara wa kananan jami’an hukumar kimanin dubu daya da dari takwas da casa’in da tara (1,899) girman mukami zuwa mataki na gaba.
Sanarwar da ta fito daga jami’in yada labarai na hukumar, DCI Sunday James ta bayyana cewa shugaban ya amince da karin girman ne bayan an samu sakamakon atisayen karin girma da aka yi wa kananan jami’an watan Nuwambar nan na 2018.
Sanarwar ta bayyana kididdigar wadanda aka kara wa girman dalla-dalla, wadanda suka kunshi Mataimakan Sufeto na biyu (AII) da aka kara wa girma zuwa Sufeto na biyu (II) su 13, da masu mukamin ‘SIA’ da aka kara wa girma zuwa ‘CIA’ su 594. Sauran su ne masu mukamin ‘IA1’ da aka kara wa girma zuwa ‘SIA’ su 949, da masu mukamin ‘IA2’ da aka kara wa girma zuwa ‘IA1’ su 329 da kuma na karshensu masu mukamin ‘IA3’ da aka kara musu girma zuwa ‘IA2’ su 14. Baki daya idan aka hada jimillarsu za su ba da adadin 1,899.
Sanarwar ta ce, a yayin da shugaban hukumar, Babandede ke taya jami’an murna, ya yi kira gare su su kasance masu biyayya ga kasarsu ta gado, Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya da suke wa aiki.
Har ila yau, ya hore su da su kauce wa tsunduma cikin duk wata harka ta cin hanci da rashawa tare da nuna da’a da bin ka’idojin aiki a koyaushe.

Exit mobile version