Connect with us

LABARAI

NIS Ta Shiga Sahun Mashahuran Hukumomi 50 Na Kasar Nan

Published

on

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) a karkashin shugabancin CGI Muhammad Babandede MFR, ta sake samun tagomashi sa’ilin da shahararriyar mujallar nan ta ‘Signature 50’ ta lissafa ta a cikin manyan hukumomin gwamnati guda 50 da suka fi shahara a kasar nan.

A cikin kwafin mujallar da aka yi nazarin shahararrun hukumomin 50, an wallafa tattaunawar da aka yi da CGI Babandede a kan muhimman batutuwa musamman wadanda suka shafi aiwatar da tsarin Bizar Nijeriya na shekarar 2020.

Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede MFR

 

Mawallafin mujallar bai yi koro ko coge wajen gabatar da mujallar ba wacce aka sadaukar da ita ga cikar Nijeriya shekara 60 da samun ‘yancin kai. Mujallar ta yi bayani dalla-dalla game da mashahuran hukumomin kasar nan 50 da suka mori kwararrun shugabanni da suka san aiki; farin sani.

CGI Babandede ya shiga sahun farko a cikin shugabannin hukumomin da suke da kwarewar aiki bisa la’akari da manyan ayyuka na ci gaba da NIS ta kaddamar domin kawo sauye-sauye masu ma’ana a bangaren Fasfo, Biza, Kula da Shige da Ficen Baki, Tsaron Iyakokin Kasa da kuma tabbatar da bin ka’ida a bakin aiki.

 
Advertisement

labarai