ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

by Abubakar Sulaiman
1 hour ago

Ƙungiyoyin ƙwadago na jihohi sun fara matsa wa gwamnonin jihohinsu lamba domin su amince da biyan ma’aikata tallafin sufuri naira 70,000 a kowane wata, bisa tsarin da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi na tsawon watanni shida, daga Nuwamba 2026. Wannan mataki ya biyo bayan yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma da Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa ga ma’aikata.

A Jihar Legas, shugabar NLC ta jihar, Agnes Sesi, ta ce ƙungiyar za ta nemi gwamnatin jihar ta biya ma’aikata tallafin naira 100,000 a kowane wata, bisa la’akari da tsadar sufuri, gidaje da abinci a jihar. Ta ce idan gwamnati ba za ta iya ƙara adadin tallafin ba, bai kamata ta biya ƙasa da naira 70,000 da aka amince da shi a matakin tarayya ba. Ta kuma buƙaci a fara biyan tallafin ba tare da jinkiri ba, domin kada ya taru ya zama bashi.

A Kaduna, shugaban NLC na jihar, Ayuba Magaji, ya ce ƙungiyar za ta rubuta wa Gwamna Uba Sani domin fara tattaunawa kan biyan aƙalla naira 70,000 ga kowane ma’aikaci a kowane wata. Ya ce wannan adadi ne farkon tattaunawar, kuma ƙungiyar za ta nemi ƙarin kuɗi idan ƙarfin tattalin arziƙin jihar ya ba da dama. A Binuwai kuwa, shugaban NLC na jihar, Terungwa Igbe, ya ce ƙungiyar za ta dage kan biyan adadin da aka amince da shi, duk da cewa gwamnatin jihar ta ce ba ta fara tattaunawa ta musamman kan batun ba.

ADVERTISEMENT

A Kebbi, NLC ta fara neman goyon bayan ƴan Majalisar Dokokin jihar domin tabbatar da biyan tallafin da zai kasance tsakanin naira 40,000 da 70,000, gwargwadon ƙarfin kuɗin gwamnati da nau’in ma’aikata. A Bayelsa, ƙungiyar ta ce bai kamata a ware jihar daga shirin ba, yayin da ƙungiyoyin ƙwadago a Ondo, Edo, Ribas, Gombe da Neja suka bayyana shirinsu na tattaunawa da gwamnatocin jihohinsu kan aiwatar da tallafin.

Sai dai ba duk ƙungiyoyin ƙwadago ne suka gamsu da tsarin tallafin ba. Shugaban TUC na Jihar Ribas, Samuel Ogan, ya bayyana cewa tallafin na watanni shida kaɗai ba zai magance matsalar tsadar rayuwa ba, don haka ya buƙaci a ƙara albashi maimakon dogaro da tallafin wucin-gadi. A Abia kuwa, NLC ta ce za ta nemi a biya tallafin na watanni shida, amma ba za ta bari hakan ya kawo cikas ga tattaunawar sabon mafi ƙarancin albashi ba.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: An Gano Mutane 2 Da Ake Zargi Na Ɗauke Da Ebola A Arewa Maso Gabas – NCDC

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

A Kano da Sakkwato, shugabannin NLC na jihohin, Kabiru Inuwa da Abdullahi Jungle, sun ce suna jiran takardar umarni daga hedikwatar ƙungiyar ta ƙasa kafin su fara tattaunawa da gwamnatocin jihohinsu. A Ogun kuwa, TUC ta ce tana tattaunawa da gwamnati kan faɗaɗa tallafin sufuri naira 10,000 da ake bai wa ma’aikatan gwamnati.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta amince da tallafin naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnati na watanni shida, amma aiwatar da shi a jihohi yana buƙatar tattaunawa da amincewar gwamnatocin jihohin.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Atiku Ya Yi Alƙawarin Ba Da Motoci 10 Don Yaƙin Zaɓen Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara
  • Abubakar Sulaiman
    Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

MASU ALAKA

Cutar Ebola Ta Ɓulla A Nijeriya
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: An Gano Mutane 2 Da Ake Zargi Na Ɗauke Da Ebola A Arewa Maso Gabas – NCDC

October 31, 2026
Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su
Labarai

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

October 31, 2026
An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara
Manyan Labarai

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

October 31, 2026
Next Post
Cutar Ebola Ta Ɓulla A Nijeriya

Da Ɗumi-ɗumi: An Gano Mutane 2 Da Ake Zargi Na Ɗauke Da Ebola A Arewa Maso Gabas - NCDC

LABARAI MASU NASABA

Cutar Ebola Ta Ɓulla A Nijeriya

Da Ɗumi-ɗumi: An Gano Mutane 2 Da Ake Zargi Na Ɗauke Da Ebola A Arewa Maso Gabas – NCDC

October 31, 2026
NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

October 31, 2026
Ɗan Atiku Ya Yi Alƙawarin Ba Da Motoci 10 Don Yaƙin Zaɓen Tinubu

Ɗan Atiku Ya Yi Alƙawarin Ba Da Motoci 10 Don Yaƙin Zaɓen Tinubu

October 31, 2026
Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

October 31, 2026
An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

October 31, 2026
Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

October 31, 2026
Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

October 31, 2026
Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

October 31, 2026
Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

October 31, 2026
Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

October 31, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.