ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗan Atiku Ya Yi Alƙawarin Ba Da Motoci 10 Don Yaƙin Zaɓen Tinubu

by Abubakar Sulaiman
2 hours ago

Abba Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin bayar da motocin bas guda 10 domin taimaka wa yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027. Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai shalƙwatar jam’iyyar APC da ke Abuja ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026.

Abba, wanda ya kafa ƙungiyar Haske Bola Tinubu Organisation (HBTO), ya samu tarɓa daga Mataimakin Shugaban APC na Arewa, Bukar Dalori. A cewar wata sanarwa da babban mai taimaka wa mataimakin shugaban jam’iyyar kan harkokin wayar da kan matasa, Yusi Buba, ya fitar, Abba ya kuma bayyana goyon bayansa ga shugabancin Tinubu da ci gaba da mulkinsa bayan zaɓen 2027.

Sanarwar ta ce motocin bas ɗin guda 10 za su taimaka wajen jigilar masu goyon bayan Tinubu da kuma gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a. Abba ya ce ƙungiyarsa za ta fara shirin tallafin sufuri ne a Babban Birnin Tarayya, Abuja, kafin ta faɗaɗa shi zuwa sauran jihohin ƙasar.

ADVERTISEMENT

Baya ga motocin, Abba ya bayyana shirin gudanar da gangamin tattara magoya baya na mutum miliyan biyu a faɗin shiyyoyin siyasa shida na Nijeriya, wanda za a fara daga Abuja. Ya kuma ce ƙungiyarsa na shirin ƙaddamar da babban gangamin siyasa a Jihar Ribas a makon farko na Nuwamba, tare da gina rassanta a sassa daban-daban na ƙasar.

Matakin Abba ya zo ne bayan ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a watan Janairun 2026, inda ya bayyana goyon bayansa ga takarar Tinubu a karo na biyu. Wannan matsaya ta sa ya kasance a wani ɓangaren siyasa daban da mahaifinsa, Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.

LABARAI MASU NASABA

INEC: Matsayin Takarar Pantami, Gwarzo Da Adebutu; Wane Sakamako Ne Zai Iya Biyo Baya?

INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

Da yake bayyana dalilin matsayarsa, Abba ya ce ra’ayin siyasa zaɓin mutum ne da ya kamata ya kasance bisa lamirinsa da fahimtarsa, ba wai dangantakar iyali ba. Ya ce kowane mutum na da ƴancin zaɓar jam’iyyar ko ɗan takarar da yake goyon baya, kamar yadda ya kamata a mutunta ra’ayoyin waɗanda suka zaɓi wata hanya ta daban.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara
  • Abubakar Sulaiman
    Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

MASU ALAKA

INEC: Matsayin Takarar Pantami, Gwarzo Da Adebutu; Wane Sakamako Ne Zai Iya Biyo Baya?
Siyasa

INEC: Matsayin Takarar Pantami, Gwarzo Da Adebutu; Wane Sakamako Ne Zai Iya Biyo Baya?

October 29, 2026
INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI
Siyasa

INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

October 28, 2026
Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa
Siyasa

Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa

October 28, 2026
Next Post
NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

LABARAI MASU NASABA

Christine Lagarde: Yadda Kasar Sin Ta Samu Nasarar Rage Talauci Abin Burgewa Ne

Christine Lagarde: Yadda Kasar Sin Ta Samu Nasarar Rage Talauci Abin Burgewa Ne

October 31, 2026
Cutar Ebola Ta Ɓulla A Nijeriya

Da Ɗumi-ɗumi: An Gano Mutane 2 Da Ake Zargi Na Ɗauke Da Ebola A Arewa Maso Gabas – NCDC

October 31, 2026
NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

October 31, 2026
Ɗan Atiku Ya Yi Alƙawarin Ba Da Motoci 10 Don Yaƙin Zaɓen Tinubu

Ɗan Atiku Ya Yi Alƙawarin Ba Da Motoci 10 Don Yaƙin Zaɓen Tinubu

October 31, 2026
Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

October 31, 2026
An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

October 31, 2026
Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

October 31, 2026
Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

October 31, 2026
Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

October 31, 2026
Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

October 31, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.