Kwamishinan Ƴansandan Jihar Zamfara, CP Muhammad Bello, ya tabbatar da kuɓutar da malaman addinin Musulunci uku daga cikin mutum shida da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar tun ranar 12 ga Satumba, 2026.
Bello ya bayyana hakan ne yayin ganawa da wasu manema labarai a Gusau ranar Juma’a, inda ya ce an kuɓutar da malaman ne sakamakon haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da rundunar ƴansanda.
Rahoton ya ce an sace malaman ne a lokacin da suke tafiya zuwa Talata Mafara domin halartar taron addu’a na musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ƴan bindigar sun tare motar da suke ciki a kan hanyar Dakko zuwa Damri, kusa da Dajin Sububu, a Ƙaramar Hukumar Bakura, da misalin ƙarfe 11:30 na safe.
Daga cikin malaman da aka ambata akwai Imam Yahuza, da Magawata Abdullahi, da Malam Shehu Dakko, da Imam Bala Fagon da Na’ibi Tasi’u.
Rahotannin sun ce masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa naira miliyan 30 domin sakin waɗanda suka sace. Wani jami’in tsaro da ya shiga aikin ceton ya tabbatar da cewa an kuɓutar da malaman ukun ba tare da sun samu rauni ba, kuma an duba lafiyarsu bayan sun samu ƴanci.
Kwamishinan ƴansandan ya ce har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da sumame domin gano sauran malaman ukun da ke hannun masu garkuwa da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.
Ya kuma yaba da bayanan sirri da al’ummar yankin ke bayarwa, tare da kira ga jama’a su ci gaba da taimaka wa hukumomin tsaro da sahihan bayanai domin tabbatar da sakin sauran waɗanda aka sace.














