Muhammad Maitela" />

NSCDC Ta Cafke Matar Aure Da Laifin Safarar Mutane A Jihar Anambra

Rundunar tsaron jama’a ta Nijeriya (NSCDC) a jihar Anambra ta bayyana samun nasarar cabke wata mata yar kimanin shekaru 34- a duniya, Misis Nkeoma Ezuma, tare da zargin safarar jama’a.

Kwamandan rundunar NSCDC a jihar, Mista Dabid Bille, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Awka, da ranar Asabar.

Bugu da kari kuma, Billie ya shaidar da cewa an cabke Misis Ezuma, wadda ta mallaki gidan saukar da baki a yankin Agulu Ezechukwu da ke karamar hukumar Aguata a jihar, a ranar 5 ga wannan wata na Nuwamba a kauyen Agulu Ezechukwu, a daidai lokacin da take kokarin cillawa kasashen wajen Nijeriya da mutanen.

Ya kara bayyana cewa, a binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa wadda suke zargin kwararriyar mai safarar kananan yara ce, tun kimanin shekaru 17 da 25 da suka gabata, inda take cefanar dasu zuwa kasar Mali hadi da sauran kasashen Afirika, yayin da ake tilasta su zuwa aikin badala (karuwanci).

Haka kuma, ya ce, rundunar su ta ceto yan mata uku daga hannun matar; Ifeoma Ezenwanne (yar shekaru 17), Chidimma Charles (yar shekaru 18) da Mmesoma Onwue (yar shekaru 17), wadanda matar ta shirya cillawa dasu zuwa kasar Mali- yawon ta-zubar.

Ya ce sun samu nasarar damke wannan mata mai safarar kananan yara yan mata ne bisa wani rahoton sirri da suka samu dangane da wannan haramtaccen kasuwanci nata, kafin a samu damar kama ta, ranar 5 ga watan Nuwamban.

Ya ce, tuni dai wadda ake zargin ta amsa cewa ta aikata wannan laifin safarar mutane, kuma tare da mika ta ga hukumar yaki da safarar mutane ta kasa: National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons (NAPTIP), bayan gudanar da binciken.

Exit mobile version