Connect with us

ADABI

Ofareshin Mu Kori ’Yar Gusau

Published

on

Mai karatu ko ka san ‘yar Gusau? To ‘yar Gusau wata yunwa ce da aka yi a yankin Gusau cikin 1934/35.  Koda ya ke a duk fadin kasar Hausa din aka yi yunwar, don ta shafo tun daga Borno zuwa Gashuwa zuwa Katsina da awasu yankunan Sakkwato da kuma Kano saboda fari da aka yi a shekarar, kuma fari su ka canye sauran abin da aka noma aka girbe. To don haka a kowanne yanki sai a kira ta ko a yi mata kirari da wani suna da ya shafi wannan yankin ko wurin. Misali, a kasar Katsina ana kiranta ‘Ta kojilo’. A kasar Gashuwa ana kiranta ‘A kyakyara’. A can yankunan kasar Zamfara ko Gusau sai aka rika ce mata ‘yar Gusau. Wannan ya sanya ma abin ya zama sara ko lakani har ya zuwa yau din nan. To da mutum ya ce ya na jin ‘yar Gusau, wai ya na nufin ya na jin yunwa kenan.

A kwanakin baya ne tsohon dan takarar gwamna a karkashin tutar jam’iyyar PDP Alhaji Umar Abdullahi Tsauri wanda aka fi sani da suna Tata ya kaddamar da abin da ya kira ofareshin yaki da yunwa a jihar Katsina. Aka kuma yi niyyar fara gwajin hakan a garin Dutsi, hedkwatar karamar Hukumar Dutsi din da ya ke a arewacin birnin Kafina, kimain kilomita 58 da rabi a tsakani. Umar Tata wanda tsohom Darekta ne a Ma’aikatar Tsaro ta kasa ya yi tasiri kwarai a jihar Katsina da ma kewayen ta a shekarar 2015 lokacin da ya yi takarar gwamnan Katsina. Zarrar da ya yi ita ce ta yawan bada kudade da abubuwan hawa kamar motoci da babura da kekuna da keke NAPEP da kayan masarufi, irin kuma kyautar mutanen da can ba irin kyautar mutanen wannan zamani ba. Kyautar mutanen zamani ita ce ta idan mutum ya zo wajen ka neman abin da ya kai darajar naira dubu 5 sai ka ba shi dubu 2 ka ce ya yi hakuri ya tafi gaba Allah Ya ba shi sauran. Su kuwa mutanen zamanin da ya shuda idan za su yi maka kyauta sai in ka na neman abjn da darajar sa ta kai naira dubu 30 to sai ma sub a ka dubu 30 din har ma da doriya, Allah bar shi idan ka yi maganin wannan matsalar ka kuma yi maganin wata matsala ta gaban wannan. Akwai ma lokutan da Tata ya rika aurar da mata a Katsina; ya yi masu kayan daki ya biya sadakin su ga ma’auratan su ya kuma ba mazajen kudin yin jail. Har ta kai ma wasu abokan hamayya su na ta nuna masa yatsu su na cewa ba ya kyautawa ya cika nuna abin da yawa.

To a rannan sai Mallam Umar Abdullahi Tsauri Tata mai dubu-dubu kamar yanda ake ce masa ya kaddamar da sha’anin yaki da fatara ko yunwa a Dutsi, kuma shirin ya yi aniyar ciyar da mabukata mata kimanin mace dubu 2. An dai yi gangami, an taru, an kuma tsara abin gwanin ban sha’awa. Mata daga ko’ina cikin karamar Hukumar Dutsi su ka taru. Masu alhakin raba abinci su ka fara rabawa. Ton Ton na hatsi da kayan masarufi aka kai cike da manyan motoci. An fara raba abincin kenan wuf sai ga ‘yan sanda da masu kare farin kaya (Cibil Defense) su ka zo su ka tarwatsa mutane sannan aka kama na kamawa. Shi kuma Alhaji Umar Abdullahi Tata aka aika masa ya tafi aka yi masa ‘yan tambayoyi a ofishin Hukumar ‘yan sanda. Satin da ya biyo bayan sa kuma sai aka tafi da shi kotu aka yi shari’a a tsakanin sa da gwamnatin jihar Katsina. Yanzu dai kura ta lafa.

A nan, daga kowanne bangare ya kamata a ce kafin yin wannan shiri an hada kai tsakanin gwamnatin Katsina da shi Umar Tata. An san cewa jama’ar kasar nan sun shiga halin da a baya ba su taba shiga ba, a ta fuskar kayan abinci. Shi dai Umar Tata, kuskuren sa da bai sanar da gwamnati ba kafin ya yi wannan yunkuri domin shi ya san ai dole ne idan a ka yi ba za a kwashe lafiya ba, ita kuma gwamnati, ko da ya ke an san cewa ba a yin gwamnati a cikin gwamnati kuskuren da ta yi da ta yi wancakali da shirin har ta aika aka kori jama’ar da ta taru a wurin. An san cewa gwamnati ita kan ta abin ya dame ta na hauhawar da tsadar kayan masarufi amma da kiran sa ta yi aka shiga yarjejeniya na kowanne bangare ya kawo tallafin sa, Allah bar shi ma ana iya hadawa da wasu masu hali na jihar Katsina kamar su Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, Alhaji Abdul’aziz mai goro, Alhaji Mannir Abukur, Alhaji Bilya Sanda. Domin kada a bar Umar Tata shi kadai saboda bambancin ra’ayi ko jam’iyya, da zaran talakawan jihar Katsina su ka ga gwamnati ta yi yekuwa ta kira wadannan da na ambata a sama, to ba za a ce zancen siyasa ya shigo ba ballantana har a yi tunanin wani abu. Sai a kira shirin da sunan shirin gwamnati na korar yunwa, don haka ga ma wasu masu hali na Jihar Katsina din an nemo su don su taimaka ma ita gwamnati din. To duk ba a duba wadannan ba.

Tun cikin shekarun (lokuta daban-daban) 1911 da 1927 da 1935 da 1943 lokacin da aka yi yunwa a kasar hausa ko kasar Katsina masu sunaye : ‘yar kumumuwa, mai kyaure, Ta kojilo, da ta baya-bayan nan mai dan buhu (ta 1943 kenan) da Sarkin Katsina Muhammdu Dikko (Zakaran gwajin dafi) ya aiwatar da shiri da yaki da yunwoyin ta hanyar saye hatsin kasar Katsina kaf ya raba wa talakawa, ba a kara yin wani shiri makamancin wannan ba sai wanda Tata ya yi a kwanakin baya. Akul, kada in kara jin wani ya yi zagi ya danganta abin da siyasa ko adawanci, wannan abu da ya yi jihadi ne kuma abin koyi ne ga sauran masu hannu da maski.

A wani bangare kuma, wasu da dama masu fassara siyasa sun ce mi ya sa Umar Tata bai nem I yin wannan shiri bat un bayan da aka yi zabe sai yanzu da za a yi zaben cike gurbin Dan majalisar Jiha? Tsakanin shirin raba abin kai wa baki na Tata a Dutsi da kuma zaben dududu bai wuce kwanaki 4 ko 5 ba. Har ma wasu da yawa na cewa ai Dutsi ba ta fi Tsauri fatara da rashin abinci ba, ya dace ya fara aiwatar da shirin a mahaifar sa kafin ya yi a Dutsi. To ko ma dai minene, a irin wannan yanayi, ba aniyar mutum ake dubawa ba, a’a amfanin abin ga al’umma ake dubawa. Tata ya taka rawar gani, kuma ya fito da kyakkyawar manufa.

Da yake masu Magana sun ce tari shi ke tado ciwon hakarkari, to wannan batu bai kamata a bar shi ba. Ina ganin gwamnati ta dawo ta kira Umar Tata Tsauri ta bashi magana sannan ta kirkiro da wani shiri makamancin wannan ta kuma kira masu hannu da maiko su zuba kudi a cikun asusu sannan a sayi hatsi a kai a raba a inda ake ganin fatara da yunwa sun fi kaifi ko naso. Da gwamnatin Jihar Katsina da bangaren ‘yan adawa da su ka fadi zabe duk dai bori daya ake wa tsafi: duk kowa so ya ke ya yi abinda za ya kyautata ma talakawan sa. To tunda an san cewa samun lamunin Dodo ke sa a shiga ruwa a fito lafiya in ji masu iya magana, mi za ya hana a nemi lamunin gwamnati kafin a aiwatar da irin wannan abin? Idan ma ba ta yarda ba an dai yi kokari. Shi Allah (SWA) aniya Ya ke dubawa.

Hakazalika wannan batu ya tuna ma ni da zamanin mulkin Firimiyan Arewa Ahmadu Bello da gwamnatin sa kan sayi kayan abinci ta raba wa talakawa. Mu na fata gwamnatocin Najeria za su assasa ko su gyara rumbunan tara hatsi don sayar ma talakawa cikin farashi kankani. Nuna wariyar siyasa ko bambancin jam’iyya shi ke sa talaka na shiga cikin halin ni-‘ya-su, halin kaka-nikayi. Ya dace a daina nuna zafin bambancin siyasa a rika hada kai, duk abin da za a yi a yi shi tare, to sai ka ga an samu sauki. Yaki da yunwa ai yin koyi ne da Sarkin Katsina Dikko kuma yaki ne na kowa da kowa ba na Tata ba ne kawai, ba na gwamnatin Katsina ba ne kawai, amma ita gwamnati ita ke da alhakin ta shirya yanda za a yaki yunwar.  Idan kuma gwamnati ba ta yi yaki da yunwa tun yanzu ba da hatsi ya ke gagarar talaka saye, to abin da ake gudu kada shi talaka ya yi yaki da gwamnati saboda ta ki matsa ma ‘yan kasuwa su sassauta farashin hatsi. Bai kamata a dube shi a matsayin adawar siyasa ba, don ya wuce wannan matsayin.
Advertisement

labarai