Oshiohmole Ya Jaddada Bukatar Sake Fasalin Jagorancin Majalisar Kasa

Jam’iyyar APC ta dage a kan cewa, tilas ne ga jam’iyyar da take da mafiya rinjaye a wakilan majalisar da aka zaba a zaman majalisar na 9, da kar su bari ‘yan adawa su karbe shugabancin mahimman mukamai.
Shugaban jam’iyyar ta APC na kasa, Adams Oshiomhole ne ya bayyana hakan a wajen liyafar cin abincin dare da shugaban kasa Buhari ya shiryawa dukkanin sabbi da tsaffin wakilan majalisar ta Dattawa da kuma wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar a fadar ta shugaban kasa da ke Abuja, ranar Litinin.
Shugaban na APC ya bayyana cewa, makasudin shirya liyafar shi ne a tsara yanda za a yi da batun shugabancin majalisar, domin tabbatar da ba a sanya ‘yan adawa a mahimman mukaman majalisar ba a wannan karon.
Ya bayyana cewa, jam’iyyar wacce take da rinjayen kimanin Sanatoci 65 da kuma wakilai 223 a majalisar wakilai ta tarayya daga cikin su 360, tana da ikon daukan duk wata shawara ba tare da tilas sai ta sami goyon baya daga ‘yan adawa ba.
“Daya ne kadai daga cikin ‘yan majalisun 16 da suka fice daga jam’iyyarmu ya ci zabe, haka Allah Ya so ya hukunta mana su.
“Akwai bukatar mu yi dubi da kyau domin mu dauki darasi mai kyau a kan abin da ya faru a shekarar 2015. A wannan karon mahimman mukamai na mahimman kwamitoci wanda a baya suke a hannun ‘yan adawa, yanzun za mu tabbatar da suna hannun jama’armu ne.
“Don haka, yana da mahimmanci mu zauna da kai a matsayin ubanmu (Shugaba Buhari), mu tattauna yanda shugabancin majalisar ya kamata ya kasance.
A kan Sanata Ifenyi Ubah, wanda yana cikin sabbin ‘yan majalisar dattawan da aka zaba a wajen liyafar, Oshiomhole, ya kwatanta shi da cewa, shi dan siyasa ne mai wayo a kan yanda ya shiga jam’iyyar ta APC.
An zabi Ubah ne a ranar 23 ga watan Fabrairu, a karkashin inuwar jam’iyyar YPP, kafin daganan ya shelanta ficewarsa daga jam’iyyar da kuma komawarsa jam’iyyar ta APC, a kwanan nan.
Daga cikin wadanda suka halarci liyafar akwai shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiohmole; Sakataren Gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha da sauran mataimaka a fadar ta shugaban kasa.
Hakanan, Gwamnonin Jihohin Kogi, Jigawa, Oyo, Kaduna, Kebbi, Zamfara, Borno, Yobe, Filato, Osun da Lagos duk sun halarta.
Zababbun Sanatocin da aka zaba sun hada da duk wadanda suka nuna aniyarsu kai tsaye ko a fakaice na neman a ba su shugabancin majalisar ta Dattawa a zaman majalisar na 9.
Shahararru daga cikin su masu neman shugabancin majalisar sun hada da, Ahmed Lawan, Danjuma Goje da Ali Ndume, duk daga sashen arewa maso gabas na kasar nan da Abdullahi Adamu, daga sashen arewa ta tsakiya.

Exit mobile version