Connect with us

MANYAN LABARAI

Pantami Ya Karyata Zargin Siyan Gidaje Uku A Abuja

Published

on

Ma’aikatar sadarwa ta Nijeriya ta zargin da wata jaridar intanet ta wallafa inda ta yi zargi cewa Minista Ali Isa Pantami ya saya wa matanshi uku gidaje a tsakiyar birnin tarayya Abuja.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Uwa Suleiman ta fitar ta ce; wannan zargin ba shi da tushe balle makama. Sanarwar ta kara da cewa: Labarin da jaridar intanet ta Sahara Reporters ta wallafa da ke zargin cewa ministan ya saya wa matansa uku gidaje a tsakiyar Abuja shaci-fadi ne kawai.

“Tun da ministan ya kama aiki a bai sayi gida ko daya ba, kuma gidan da yake zaune ciki ya kama shi ne tun a watan Janairun shekara 2017, shekara biyu kenan kafin ya kama aiki”, in ji sanarwar.

Ta kara da cewa sauran gidaje biyun da jaridar ta wallafa bai ma san daga inda ta samo su ba. Bugu da kari ta yi kira ga al’ummar kasar da su yi watsi da wannan kokarin na bata wa Minista Ali Pantami suna da ake kokarin yi.

 
Advertisement

labarai