Kalu Eziyi, " />

PDP Na Gab Da Karewa A Yankin Igbo, Inji Apugo

Prince Benjamin Apugo

Jagoran Jam’iyyar APC a jihar Abia, Prince Benjamin Apugo ya shelanta cewa, jamiyyar PDP a Kudu maso Gabas na gab da bacewa, inda ya kara da cewa, jam’iyyar ba ta taba yin fatan alheri ga jama’a ba.

Apugo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bukuncin kwamitin sake sabunta katin yayan APC a gidansa da ke a Karamar Hukumar Umuahia.

Ya kuma kalubalanci PDP a jihar wacce ke rike da madadun ikon jihar tun da ta dare kan karagar mulkin jihar kan gazarawrta na cika alkawuranta na yakin nemamn zabe a jihar duk da goyon bayan jama’ar jihar da ta samu a baya.

Apugo wanda kuma ya kasance daya daga cikin jigogin APC na kasa ya yi amfani da damar wajen yin watsi da ikirarin da wasu ke yi cewa, shugaba Muhammadu Buhari bai yiwa yan kabilar Ndigbo adalci ba wajen bayar da mukamai ba.

Ya gode wa kwamitin kan zuwa Jihar tare da yaba wa shugaban kasa kan nada sabon shugaban tsaro na soji Majo Janar Leo Irabor Igbo da ya fito daga jihar Delta.

Ya kuma yi kira ga yayan jamiyyar da ke a shiyyar da su yi amfani da damar aikin domin daidaita banbance dake a tsakanin yayan jamiyyar, musamman domin samar wa da Jamiyyar alkibla a zaben kakar shekarar 2023 domin fafata wa da PDP a shiyyar.

A jawabinsa tunda farko, shugaban kwamitin Jakada Bala Mohammed Mairiga, ya danganta Apugo a matsayin daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki na jamiyyar a kasar nan da kuma damar da samar a yi rijistar a gidansa.

Ya bayyana cewa, aikin wanda za a gudanar da shi a ranar Talata, ba wai za a yi shi domin cin zarafin yayan jamiyyar ba ne, amma zai bai wa tsofaffi da sabbin da za’a su sabunta wa kuma your n rijista domin tunkarar zaben 2023.

 

Exit mobile version