Connect with us

LABARAI

PDP Ta Yi Allah Wadai Da Zaftare Wa Ma’aikata Albashinsu A Bauchi

Published

on

Babban Jam’iyyar Adawa ta PDP a jihar Bauchi ta nuna takaicinta da kuma yin Allah wadai da zaftare wa wasu ma’aikatan Bauchi Albashinsu na watan Mayun da gwamnatin jihar ta yi.

Da yake ganawa da manema labaru a Bauchi, Kakakin Jam’iyyar PDP a jihar ta Bauchi Alhaji Yayanuwa Zainabari ya cewa matakin da gwamnatin jihar ta dauka abun babu dadi domin hakan ya jefa wasu ma’aikatan cikin kunci a sakamakon rage masu wani kaso daga albashinsu a maimakon gwamnatin ta kara musu.

Zainabari ya yi zargin cewar gwamnatin ta kaza daukan sabbin ma’aikata don haka ba daidai ba ne wadanda suke dan fama da aikinsu suma ake samun irin wannan matsalar da ka iya jefa su cikin yanayi na rashin jin dadi da walwala.

Zainabari ya ce su a lokacin da suke mulki ma’aikata sun yi walwala sosai, “Lokacin da mu PDP muke kan karagar mulkin jihar, abun da muke yi wa ma’aikatan gwamnati shi ne kara musu albashinsu a kowani lokaci domin kyautata aikin, mun kuma dauki ma’aikata sosai a lokacin da muke mulkin jihar. Idan gwamnan ya fito ya ce babu kudin da zai biya ma’aikata ko kuma babu sararin sake daukan sabbin ma’aikata a jihar, sai mu jefa masa tambaya da cewar mu a ina muke samo kudin da muke biyan ma’aikata kudinsu mu kuma dauki karin ma’aikata?,” Kamar yadda ya tambaya.

Yayanuwa Zainabari ya shaida cewar a irin wannan lokacin da jama’a ke neman kudi domin gudanar da bukukuwan sallah sam bai kamaci gwamnati ta rage wa ma’aikata albashinsu ba, yana mai bayanin cewar kara musu ne ma ya kamata gwamnatin ta yi na ragewa ba.

Daga nan kuma, Kakakin Jam’iyyar PDP a jihar sai ya bukaci dukkanin jama’an jihar Bauchi da su yi umumu su fara shirin dangwala wa jam’iyyar PDP kuri’unsu a zaben gwamnan jihar da ke tafe domin su samu zarafin shimfida aiyukan alkairi a jihar.

Sai dai kuma a ranar Litinin ne gwamnatin jihar Bauchi ta shaida dalilanta da suke sabbaba ta zaftare wa wasu ma’aikata Alawus dinsu na watan Mayu, inda suka bayyana cewar wasu ma’aikatan suna daukan abun da bai kamacesu su dauka ba.

Darakta a sashin kula da tsare-tsare na ofishin shugaban ma’aikatan Bauchi Alhaji Isyaku Tijjani shi ne ya yi magana a madadin shugaban ma’aikatan Bauchi, ya ce wasu ma’aikata da dama basu samu albashinsu ba na watan Mayu hakan kuma ya samo asali ne daga matsalar nan ta fara amfani da sabon tsarin da suka fara na biyan albashi, yana mai shaida cewar kowani ma’aikacin da bai samu albashinsa za su bincika kuma za su biyashi hakkinsa.

Dangane da matsalar zaftare wani kaso ga ma’aikata kuwa, Tijjaniya ya shaida cewar sun yi zaftarewar ne kadai akan Alawus din ma’aikatan jihar, ya kuma shaida dalilinsu na yin hakan.

Ya ce; “Wasu mun lura suna amsar Alawus din da a gaskiya ba sune ya kamata su amshi wannan adadi na alawus din ba. kuma wasu suna amsar alawus din fiye da yadda ya kamata a basu. Wasu kuma masu karban alawus din nan suna amsa ne amma babu takarda daga gwamnati da ta amince a amshi wannan alawus din. Wadannan ne aka ciccire,” In ji Daraktan.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: