Gabanin zaben 2027, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a shekarar 2023, Peter Obi, ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da sauran hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da sahihancin takardun shaidar karatun ‘yan takara kafin su amince musu shiga zabe a 2027, domin kaucewa rudani lokacin da aka zabe su.
Ya kara da cewa yawancin masu rike da mukaman gwamnati a yau suna bayyana takardun shaidar karatu na bogi, wanda suka yi amfani da su a zaben 2023 tare da wucewa tantancewar INEC da na jami’an tsaro da kuma na majalisar dattijai duk da takardun bogi.
- Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
- Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos
Obi ya bayyana hakan ne a safinsa na Tuwita a ranar Litinin.
Ya ce, “Ina mai kira ga hukumar INEC ta tabbatar da takardun karatun duk wani mai neman mukamin shugaban karamar hukuma ko dan majalisar jiha ko gwamna har zuwa shugaban kasa, domin yin amfani da takardun karatu na bogi babban laifi ne a kowacce kasa a duniya.
“Lallai dole ne INEC ta tabbatar da cewa ‘yan takara sun gabatar da sahihin takardun karatu kafin a amince su shiga zabe, domin kaurace wa korafe-korafe lokacin da matsalolin zabe suka kunno kai a kotu, wanda tun kafin shiga zaben za a kori mai takardun bogi tare da hukunta shi daidai da laifin da ya aikata.
“Ko bayan kammala zabe, INEC ba ta damu da binciken wannan babbar matsala ba domin kawo gyara a zabe na gaba.
“A yanzu muna fuskantar zaben 2027, INEC tana da isasshen lokacin gudanar da binciken korafe-korafen da aka samu a zaben da suka gabata na yin amfani da takardun karatun bagi da sauran wasu karyayyaki da ‘yan takara suke yi.
“A wurin gyaran dokar zabe, ya kamata a shigar da cewa duk wanda zai tsaya takara ya gabatar da sahihian takardunsa tun kafin wata shida kafin zabe.
“Ya kamata a yi haka ga duk wadanda za a bai wa mukaman gwamnati da suka hada da minista da masu bayar da shawara domin tsaftace harkokin gudanar da gwamnati.
“Ta wannan hanya ce za a iya kawo karshen yin amfani da takardun karatun boge tare da hukunta wadanda aka kama domin ya zama izina ga masu kokarin yin haka a nan gaba,” in ji shi.