Pogba Dan Wasa Ne Na Musamman — Mourinho

Daga Abba Ibrahim Wada

 Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Paul Pogba dan wasa ne na musamman kuma yanada tasiri babba a kungiyar.

Mourinho ya bayyana hakane a yayin hirarsa da manema labarai bayan kungiyarsa ta tashi daga wasan data doke Newcastle United daci 4-1 a wasan gasar firimiya wasan mako na 12 a filin wasa na Old Trafford.

Pogba dai ya shafe makonni tara baya wasa sakamakon ciwo dayaji a cinyarsa bayan dan wasan yafara buga wasan firmiya da kafar dama kafin yatafi jiyya.

Pogba shima yasamu dammar zura kwallo a raga a jiya bayan kuma ya taimakawa dan wasa Martial ya zura kwallon farko da United din taci.

Mourinho ya ce, Pogba dan wasane na musamman kuma abin alfahari domin tun lokacin da dan wasan yaji ciwo kungiyar ta samu nakasu wajen cin wasanni.

Ya ci gaba da cewa dawowar dan wasan zata taimakawa kungiyar sosai wajen ci gaba da zura kwallaye a raga sannan kuma yan wasan kungiyar zasu samu kwarin gwuiwa.

Dan wasan gaba na kungiyar, Zlatan Ibrahimobic shima yadawo bayan yayi watanni 8 yana jiyya kuma yabuga wasan da kungiyar ta buga a jiya sai dai takwaransa Marcos Rojo bai samu dammar buga wasa ba duk da shima yana cikin yan wasan benci da Mourinho ya fita dasu wasan.

Manchester United zata buga wasanta na gaba a gasar zakarun turai da kungiyar kwallon kafa ta FC.Basel ta kasar Switzerlan a tanar Laraba kafin kuma ta karbi bakuncin Brighton Albion a wasan firimiya a mako mai zuwa.

 

Exit mobile version