Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Pompeo Mai Kyamar Baki Yana Zubar Da Kimar Amurka A Idon Duniya

Published

on

Kwanan baya, tashar yanar gizo ta jaridar New York Times ta wallafa wani rahoto mai taken “Pompeo ya sa ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ji kunya”, inda aka bayyana cewa, Mike Pompeo ya bata sunan ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka wanda a baya ke da kima bayan namijin kokarin da aka yi a cikin daruruwan shekaru da suka gabata, tsokacin da sakataren harkokin wajen Amurka ya yi ya jefa tsarin diplomasiyyar kasar a cikin mawuyacin yanayi.

Kwanan baya hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD ta zartas da wani kuduri, inda aka nada babban jami’in kula da harkokin kare hakkin dan Adam Michelle Bachelet da ya jagoranci aikin binciken manufar wariyar launin fata ta hukumomin da abin da ya shafa na kasashe daban daban, duk da cewa ba a ambaci batun wariyar launin fata na Amurka ba, amma Pompeo ya soki kudurin, wai yana da rauni, har ya bayyana cewa, ya dace hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD ta kara mai da hankali kan wariyar launin fata a kasar Sin, tsokacinsa ya bai wa al’ummun kasa da kasa mamaki matuka.
Hakika ba mai yiyuwa ba ne a boye ainihin yanayin wariyar launin fata da Amurka ke ciki, wasu kafofin watsa labarai sun nuna cewa, kila zargin kasar Sin ba sabon abu ba ne ga Pompeo.
A fili yake cewa, dalilin da ya sa Pompeo ya yi haka shi ne domin nuna biyayya ga shugabannin kasarsa, jaridar New York Times ta soke shi cewa, matakan da Pompeo ya dauka ya sa Amurka ba ta taka rawa ko kadan yayin da daukacin kasashen duniya suke fuskantar rikici mai tsanani tun bayan shekarar 1945.
Yadda Pompeo ya dauki matakan zargin wasu kasashe da shara karya yadda yake so, sun bata muhimmin lokaci na Amurka yayin da take dakile annobar cutar COVID-19, haka kuma suna zubar da kimar Amurka a idon duniya.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Advertisement

labarai