Rabiu Ali Indabawa">

Rago Mafi Tsada Da Aka Taba Sayarwa A Duniya A Kan Naira Miliyan 190

Wani Rago da wasu iyalai suka kiwata a garin Stockport dake Ingila ta janyo cece-kuce. An yi gwanjonta inda aka sayar da shi a kan kudi har Dalar Amurka 490,000 wanda daidai yake da Naira 190,000. Irin Ragon mai suna Tedel a halin yanzu shi ne mafi tsada a fadin duniya. Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa. Ragon mai suna Diamond an sayar da shi a makon nan bayan Charlie Boden da iyalansa sun yi kiwonsa a gonarsu ta Mellor Hall.

A yayin gwanjon Ragon da aka yi, an fara da taya shi a kan Dalar Amurka 9,000 amma babu jimawa aka kaita har Dala 490,000.

Wasu manoman ‘yan kasuwa ne suka sayi dabbar inda suke so su raineta tare a gonarsu domin samun irinta. Kungiyar kula da tumakin irin Tedel, ta ce wannan ta karya tarihin da wata tinkiyar ta kafa a 2009 wacce aka siyeta a kan kudi har pam 231,000.

Advertisements

Kamar yadda kungiyar ta sanar, an fara samun irin wannan dabba Tedel ne a wani tsibiri mai suna Tedel, wanda daya ne daga cikin tsibirran Holland, amma yanzu tumakin Ingila sun mamaye yankin. Jeffe Aiken, daya daga cikin manajojin gonar Procters, kuma daya daga cikin masu bukatar sayan dabbar, ya ce: “A tun farko dai Tedel su ne irin tumaki mafi kyau a Ingila. In kana son tumaki masu matukar nagarta, ka gwada sayansu. “Dabba ce daban ba irin kowacce ba. A cikinsu wannan ce mafi nagarta da na taba gani. Muna fatan zai kasance hakan.”

Exit mobile version