Daga Abdulrazak Yahuza Jere, Abuja
Kungiyar Matasa Musulmi na Rukunin Gidajen ‘Yanmajalisar Tarayya da ke Unguwar Apo a Babban Birnin Tarayya Abuja (NAKYMF), ta gudanar da taron lacca da addu’o’i domin samun koshin lafiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Addu’o’i wanda har ila yau suka kunshi rokon Allah don samun dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya, sun gudana ne a Masallacin Jumma’a na Rukunin Gidajen ‘Yanmajalisar Tarayya da ke Unguwar ta Apo a Abuja.
Da yake gabatar da lacca wacce ta fi mayar da hankali a kan matasa, Babban malamin da aka gayyata, Limamin Shalkwatar Rundunar ‘Yansanda ta Kasa, Imam DSP Ahmad Adam Kutubi, ya ce rayuwar matasa Musulmi ta shiga wani hali a yau a duniya saboda yadda wasu mutane shaidanu ke yakar tunaninsu daga barin addini zuwa shagalta da rayuwar sha’awa ta duniya.
Ya yi wa LEADERSHIP Hausa karin haske kan muhimman batutuwan da laccar ta kunsa.
“Wannan laccar manufarta ita ce zaburad da matasa su dubi rayuwarsa su ga shin me suka yi wa addini. Kuma wani abu ne zai zama alamar da suka bari wanda ko bayan ba su nan zai taimaka wa al’umma, da kasa da ma rayuwarsu ta duniya da lahira baki daya. A karkashin wannan akwai tambayoyi guda biyu, na farko me suka yi wa addininsu? Na biyu me suka gabatar a rayuwarsu da za a gani a ce lallai sun cimma nasarar rayuwa? Shi ya sa muka ga ya dace a samu matattarar matasa kamar wannan Masallacin na Zone E wanda ‘centre’ ce da ta karbu a wurin matasa”.
Malamin ya ce domin karfafa wannan yunkuri nasu, sun wallafa littafai guda biyar domin raba wa matasan. Ya bayyana abubuwan da littafan suka kunsa.
“Daya daga cikin littafan yana magana ne “ina matasa?”, ya yi magana a kan halaye nagari da ya kamata matasa su karba. Sannan ya yi magana a kan komawa ga Allah sannan matasan su san cewa rayuwa ta dindindin ita ce rayuwa ta Allah, duk abin da ka tara ko kake da shi dole wata rana za ka koma kabari, a ciki ba ka da komai sai abin da ka aikata a nan duniya. Allah a cikin Alkur’ani, Suratu Yasiyn, ya ce ya aiko da Manzon Allah (SAW) ne don ya yi gargadi ga mutanen da ko iyayensu ba su samu mai masu gargadi ba suna cikin shagala. To shi ya sa muka ga ya dace mu zaburad da matasa su farka daga barcin da suke yi”.
Imam DSP Ahmad, ya yi tsokaci kan rayuwar Manyan Sahabban Manzon Allah (SAW) da ya ce akwai bukatar kowa ya yi nazari a kai tare da yin koyi da su.
“Sayyidina Abubakar (RA) ya taimaki Manzon Allah (SAW) a lokacin da kafiran Makka suka matsa masa har ma Allah ya ce masa “na biyun-biyu”. To mu yi nazari me Sayyidina Abubakar ya yi ya kai ga samun wannan shaida daga Ubangiji da aka gwama shi da Manzon Allah (SAW) ya zama kamar shi ne waziri? Shi ma Sayyidina Umar (RA) Annabi ya ba da shaida a kansa cewa “da a bayana akwai Annabi da Umar ne”. Matasa sai mu duba mu ga yaya Umar ya rayu, da halinsa, da dabi’unsa har ma a duniya ake lissafa shi daga cikin masu adalci ya kuma zamo katanga ga Musulunci da Musulmi alhali kafin musuluntarsa mai tsananin adawa ne da addinin?
“Haka shi ma idan muka duba Sayyidina Usman (RA) mai tsananin kyauta. Wata rana ya sayo rakuma dubu dauke da kaya suka shigo Makkah. Mawadatan Makkah suka nemi ya sayar musu suka ninninka masa riba har sau hudu amma ya ce ba zai sayar masu ba. Ya ce masu Allah ya saya da riba ninki goma, ko akwai wanda zai saya sama da haka? Suka ce a’a, sai ya ce a je a raba wa talakawa miskinai saboda Allah. Ka ga matashi idan ya ji wannan kuma yana da dukiya ai zai yi koyi da Sayyidina Usman. Manzon Allah (SAW) ya ce Allah da Mala’ikun Rahama suna jin kunyar Sayyidina Usman kuma shi ne ‘zunnurain’ saboda ya auri ‘ya’yan Manzon Allah (SAW) guda biyu. Haka kuma idan muka dauko rayuwar Sayyidina Aliyu (RA) za mu ga shi matashi ne a zamanin Manzon Allah (SAW) amma mutum ne jarumi mai kwazo. Shi ne yaro na farko da ya fara yin mubaraza a Yakin Badar. A Yakin Gwalalo (Gazwatul Ahzab), an kewaya Madina da rami, sai wani kafiri Amru bin Widdun ya tsallako, Sayyidina Aliyu ne ya tari gabanshi. Ya ce ma Sayyidina Aliyu ya koma a turo wani mai shekaru ya zo don babansa abokinshi ne. Sayyidina Aliyu ya ce masa nine daidai da kai kuma babana ba abokinka ba ne. Bayan Sayyidina Aliyu ya kira shi zuwa ga Musulunci ya ki, ya nemi ya koma inda ya fito ya ki, sai ya ce masa to zai yake shi duk da yana kan doki shi kuma yana kan sawunsa. Suka gwabza, kura ta tashi sama Sayyidina Aliyu ya kashe shi… To haka Sahabban Annabi (SAW) suke”.
“Matasanmu sun rungumi ‘cibilization’ sosai, sai dai ya kamata su san cewa akwai hadari a ciki. Su manufar turawan rayuwa ce kawai ta zahiri, yadda mutum zai yi ya wala, ya wataya da duk abin da za ka yi ka more rayuwa. To mu kuma Musulmi ba haka ba ne, rayuwarmu biyu ce, akwai ta duniya da ta lahira”.
Ya kara da cewa musamman an fi samun hadarin juye kwakwalen matasa su shagala ta hanyar kafofin nishadantarwa na zamani da aka bullo da su wanda ko mutum bai yi boko ba zai iya amfani da su.
“Gaskiya matasa suna fuskantar kalubale ta fuskoki da yawa wurin shagaltar da su. Farko irin littafan da suke karantawa. Littafan kamar shinkafa ce aka dafa ta ji komai da komai amma kuma akwai dafi a ciki da matasa suke ci. Akwai alheri tabbas a cikin littafan ‘cibilization’ na turawan yamma sai dai akwai hadari. Allah ya ce su turawan yamma sun san zahirin rayuwar duniya, yadda za su tsara ta amma sun bar lahira. Dabi’unsu kamar sa sutura sun banbanta da irin na addini. Tsarin mu’amalarsu ya banbanta da na addini, haka manufarsu ta sha banban da ta addini. Duk abin da za mu karanta nasu mu karanta da Sunan Allah. Mu san mai kyau a ciki mu yi amfani da shi; mu san mara kyau domin mu guje shi. Haka nan kalle-kallen da za mu rika yi a ‘satellite’ da mu’amalarmu a facebook, whatsapp da sauran abubuwa. Mu rika amfani da su kuma muna tuna cewa akwai su da hadari na abubuwan da za su raba mu da Allah. Idan mun ga abubuwan da za su raba mu da imani da lahira kada mu yarda, mu karbi cigaban da ke ciki mu amfana mu watsar da wadanda za su kai mu ga halaka”.
Malamin ya ce abubuwan da ake gani na cigaban kimiyya da fasahar zamani ba bakon abu ba ne a Musulunci, “saboda Allah ya ce zai halicci abin da ba mu sani ba. Ga shi Allah ya halitta mana. To amma su turawan yamma sun dauki salon bata rayuwar matasa maza da mata. Wata budurwa Musulma kawai za ta kalli wata baturiya ce da irin suturar da ta sanya, sai ta ji sha’awa ta ce ita ma shi za ta sa koda kuwa ya ci karo da addininta. A wurinta wai wannan cigaba ne, idan iyaye sun tsawatar sai ta ce sun matsa wa rayuwarta. Idan namiji ne kuma ka ga yaro a gidan mata, gidan giya da sauran wuraren da za su lalata tarbiyyarsa”.
Wakazalika, Imam DSP Ahmad Kutubi ya ce domin rigakafin wannan lalacewa, ya kamata Gwamnati ta san cewa tana da hakkin wurin kiyaye aukuwar abin, sannan sauran jama’a kamar ‘yan jarida su yi kokarin yada wa’azozin kwararrun malamai da kuma sanya manhajar karatu da ba za ta gurbata dabi’un yara a makarantu ba.
Da yake godiya ga malamin da ya gabatar da laccar, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya bukaci matasa su karanta littafan da aka raba sannan su yi kokarin koyi da akalla guda daya daga cikin Sahabban da aka rubuta tarihinsu a daya daga cikin littafan.
A halin da ake ciki kuma, Shugaban Kungiyar Matasa Musulmi na Rukunin Gidajen ‘Yanmajalisar Tarayya, Malam Tanimu Labaran ya bukaci ‘Yan Nijeriya su dukufa ga addu’o’in samun koshin lafiyar Shuagaba Buhari maimakon karkata hankula ga yada jitajita.
A takardar sanarwar da kungiyar ta raba, shugaban ya kuma yi kira ga fadar shugaban kasa ta rika bayyana wa ‘Yan Nijeriya yanayin samun saukin shugaban kasan domin samun natsuwa. Kana ta bukaci mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi tsayuwar daka wajen aiwatar da muhimman al’amuran kasar tare da yin biris da rudanin da wadanda ba su da kishin Nijeriya ke haddasawa.