Wasu takardun Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), sun nuna cewa Hon. Bashir Machina ne ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa a Jihar Yobe.
Rahoton tawagar INEC da ta aika don sanya ido kan zaben fidda gwani da Omale Samuel, ya sanya wa hannu mai dauke da kwanan wata 28 ga Mayu, 2022, ya kuma nuna cewa Machina ya samu kuri’a 289 daga cikin kuri’a 300 da wakilan APC suka kada.
- Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi Da Karar Buhari Kan Sashe Na 84(12) Na Dokar Zabe
- Muna Da Hujjojin Magudi A Zaben Fid Da Gwanin PDP Na Kaduna Ta Tsakiya – Lauya
Har ila yau, wani rahoto daga ofishin INEC na jihar Yobe kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawan Yobe ta Arewa, ya nuna cewa an gudanar da zaben ne a gidan gwamnati da ke Gashua, hedikwatar karamar hukumar Bade ta jihar.
Gundumar ‘C’ ta kunshi kananan hukumomin Bade, Yusufari, Jakusko, Nguru, Karasuwa, da Machina.
Rahoton ya kara da cewa an fara zaben fidda gwanin da misalin karfe 11:30 na safe kamar yadda aka tsara, inda ya kara da cewa jami’an tsaro da jami’an zabe na kananan hukumomin da abin ya shafa duk sun halarta.
“Yayin da za a fara zabukan fidda gwani, dukkan ’yan takara da dukkan jami’an jam’iyyar sun hallara domin sanya ido tare da kuma wakilan jam’iyyar.
“An fara zaben fidda gwani ne da bude addu’o’i daga sakataren kwamitin tsare-tsare Alh. Lawan Modu Sheriff,” in ji rahoton.
Tikitin takarar Sanata na APC a Yobe ta Arewa ya haifar da cece-kuce bayan da wanda ya lashe zaben, Bashir Machina, ya dage cewa ba zai bar takarar ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ba, wanda a halin yanzu yake wakiltar kujerar sanatan.
Lawan dai ya tsaya takarar neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, kuma ya sha kaye a hannun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a farkon watan Yuni.
Sai dai shugabannin jam’iyyar APC na kasa sun mika sunan Lawan ga INEC domin tantance shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a Yobe ta Arewa a zaben 2023, lamarin da ya janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta.