Ali Abubakar Sadik" />

Ranar June 12 Ga Watan Yuni

Tsawon tarihi Dan Adam ya kasance ya na ba wa ranaku mahimmanci sakamakon wani gagarumin abu da ya faru a wannan rana kuma ya zama ya na da tasirin gaske a rayuwar mutane. Kama daga ranaku wadanda a ka samar da wani gagarumin abu na tarihi da mutane ke iya gani kuru-kuru, kamar gina dalar da ke Misra a shekara ta 3000 BC kafin zuwan Annabi Isa, ko kafa harsashin gina wani gagarumin gari a tarihi kamar birnin Rome a Shekarar 753 BC kafin zuwan Annabi Isa, Tsire annabi Isa a shekara ta 29 AD, Haihuwar annabi muhammadu a shekarar 570 AD da kuma Hijirarsa daga Makka zuwa Madina a shekarar 622 AD, ayyana ‘yancin Amurka daga karkashin mulkin mallaka na England a shekarar 1776, fara yakin duniya na daya a shekarar 1914 da yakin duniya na biyu a 1939 da samun ‘yancin kan Nigeria a shekarar 1960. Duk wadannan ranaku masu muhimmancin ne a rayuwar mutane don haka duk inda ka ji wata wararriyar rana ana tunawa da ita ka tabbata cewa ta na da matukar tasiri cikin rayuwar wadannan mutane.
Gwamnatin Buhari ta kafa tarihi wajen kaddama da ranar 12 ga watan Yuni ta zama wararriyar rana don tunawa da Abiola da kuma zaben shugaban kasa da ya lashe a shekarar 1993. Tun da aka ayyana wannan kuduri ake ta cece-kuce tsakanin masu goyon bayan lamarni da wadanda ba sa goyon baya. Shin wannan rana ta cancanci wannan karramawa ko kuwa a’a?
Abinda kowa ya hakkake da shi a wancan lokaci kawo yanzu shine, an yi zabe mafi karbuwa a tarihin Nigeria wanda wani dan takara ya taba samun rinjayen kuri’a daga kowanne sashe na kasar nan a shekarar 1993. Amma sai Gwamnatin soja ta wancan lokaci karkashi Janar Babangida ta soke zaben. Soke wannan zabe ya haifar da mummunar zanga-zanga da kuma halin dar-dar tare da jefa kasar cikin rashin tabbas a makomar siyasar kasar da rashin tsaro. Soke zaben ya tilastawa shi kansa Janar Babangida hakura da mulkin kasar ya dora gwamnatin rikon kwarya karkashin Shonekan wanda daga bisani Janar Abacha ya dare mulkin. Daukar mataki mai zafi game da masu zanga-zanga a sashen kudu maso yammacin Nigeria da Abacha ya yi, sakamakon ‘yan OPC sun mai da rigimar zaben ta yarbawa kawai, sai sauran kabilu su ka zame jikinsu daga fafutukar.
Wasu daga cikin jihohin yarbawa, tun daga wancan lokaci su ka ware wannan rana don yin bukukuwa da tunawa da Abiola da soke zaben. Abacha ya fafari ‘yan OPC da Nadeco yadda akasarinsu su ka tsallake gudun hijira kasashen waje. Wannan soke zabe ya zafafa yanayin siyasar Nigeria da kuma bawa yarbawa damar lallai sai sun karbi mulki daga arewacin Nigeria. A cikin manyan mutane da su ka hura wa Abacha wuta game da dawo da mulki hannun farar sun hada da Janar Obasanjo da Janar Shehu Yar’Adua. Abacha ya sa an kama duk su biyun an caje su da kokarin kifar da gwamnati ta hanyar juyin mulki kuma a ka kai su kurkuku. A watan December na 1997, sai katsam aka sanar da mutuwar Shehu Musa Yar’adua a kurkuku, mutuwar da wasu su ka yi zargin cewa an yi masa allurer cutar kanjamau ne wadda ta yi sanadiyar ajalinsa. Ana cikin wannan yanayi sai kuma katsam Abacha ya mutu ranar 8 ga watan Yuni na 1998, ita ma mutuwar da aka yi zargin cewa an bashi guba ne ya ci. Ana nan kuma kasa da wata guda da mutuwar Abacha, wato a ranar 7 ga watan Yuli na 1998 bayan ya sadu da wasu wakilai daga kasashen waje kuma ana dab da sakin sa daga inda ake tsare da shi, sai Abiola ma ya mutu. Wato a tsakanin watanni bakwai, mutanen da suka zama su ne matsalar siyasa a Nigeria duk sun tafi lahira, kuma kowannensu ya mutu a wani yanayi na abin zargi. Shin mutuwar Allah su ka yi ko kuwa duk kashe su aka yi?
Hakika mutuwar wadannan mutane uku kusan lokaci guda ya kawo sanyi a zafafar da yanayin siyasar ya yi, amma kuma sai ya dada kunno da bukatar yarbawa ta cewa lallai a basu damar dare mulkin kasar. Janar Babangida, ya sake yunkurinsa na Maradona da ya saba, da kokarin ganin ya yi amfanida wannan dama wajen harbin tsuntsaye biyu da dutse daya; wato wanke kansa a wajen yarbawa tare da amfani da damar wajen ganin ya sake dawowa mulki a karo na biyu karkashin farar hula. A tasa hikimar, sai ya yi wuf ya hada kan mutanensa ya kuma jagoranci fito da Obasanjo daga kurkuku tare da kafa jam’iyyar PDP don bashi mulki. Tsoho na Ota ya yi na’am da shawarar ya kuma tsunduma cikin yakin neman zabe, zaben da ya lashe a shekarar 1999.
A bayyane ya ke cewa a duk duniya babu wani mahaluki da ya ci gajiyar fafutukar Abiola da ranar 12 ga watan Yuni irin Janar Obasanjo. Domin ba don wannan fafutuka ba, babu ta yadda za’ayi Obasanjo ya iya tsayawa takara a 1999. Na farko dai ba don Abiola ya ci zabe an kwace ba, kuma ba don Babangida ya tashi neman bayarabe da za su mara wa baya ba, ba don sauran ‘yan Nigeria sun aminta da cewa hakika saboda abinda aka yi wa Abiola ya kamata su sakawa yarbawa da shugaban kasa ba (Dalilin da ya sa duk ‘yan takara biyu a 1999 su ka kasance yarbawa), da babu ta hanyar da Obasanjo zai dawo mulki a karo na biyu. Amma abinda zai ba ka mamaki, yarbawa a jihohin Ekiti, Lagos, Oyo, Ondo, Osun, Ogun gaba dayansu ba su zabi Obasanjo da jam’iyyarsa ta PDP ba, su ka zabi Olu Falae, shi ma bayarbe, a karkashin jam’iyyarsu ta AD. Obasanjo ya ci zabe da kuri’a miliyan 18 inda ya kada Olu Fale mai kuri’a miliyan 11. A shekara ta 2003 Obasanjo ya sake shiga zabe tare da Janar Buhari da Odumegwu Ojukwu inda ya sami kuri’a miliyan 24 shi kuma Buhari ya sami kuri’a miliyan 12 Ojukwu kuma miliyan 1. Abinda ya canza a shekarar 2003 sabanin ta 1999 shine yarbawa sun bawa Obasanjo kuri’arsu a duk jihohinsu.
Shin Obasanjo ya sakawa ‘yan Nigeria da alfarmar da su ka yi ma sa ta ba shi damar mulki a karo na biyu? Babu shugaban da ya sami damar canza Nigeria kamar Obasanjo saboda ya zo a mulkin farar hula kuma cike da goyon bayan ‘yan Nigeria da sauran kasashen waje. An sami kudin da ba’a taba samu ba daga kudaden kasar waje kafin zuwansa, sannan akwai zaman lafiya. Amma kash! Duk da cewa mulkin Obasanjo ya kawar da matsalar 12 ga watan Yuni amma ya farfado da mummunan halin banbancin kabilanci da na addini. Mun san cewa Janar Babangida shine mutumin da ya tabbatar da dorewar cin hanci tsakanin ‘yan Nigeria wajen yaudarar mutane da kudi ko mukami (kamar yadda ya yaudari irinsu Wole Soyinka da Tai Solarin d.s.s.) to amma kuma Obasanjo shine wanda ya tabbatar da cin hanci a tsarin hukumomi da ginshikan mulki. Domin mun ga yadda aka rika kai kudade a buhunan bakko don siyen ra’ayin ‘yan majalisa da yadda aka rika amfani da alkalai da wakilan jama’a wajen cire gwamnoni.
Haka kuma, shin Obasanjo ya saka wa kabilarsa ta yarbawa saboda a dalilin 12 ga watan Yuni ya sami mulki a karo na biyu? Mai karatu ka bawa kanka amsa. Abinda da na sani dai shine cewa Janar Buhari ya nuna halacci ga yarbawa yadda ba wani shugaba da ya yi musu hakan tun zaben 1999. Buhari ya nuna cewa shi dan halak ne sakamakon cewa da kuri’ar yarbawa ya hau mulki a karo na biyu, kuma ya zakulo wannan rana mai mahimmanci a tarihin kasar nan, wato 12 ga watan Yuni tare da mai da ta ranarmu ta dimlkuradiya. Wannan abu ya cancanta ba don komai ba saboda a dalilinta an rasa rayuka na fitattun yan Nigeria irinsu shi kansa Abiola da Shehu Yar’Adua ban da daruruwa da aka kashe sakamakon tashe tashen hankula na kabilanci da ya biyo baya. Wannan rana ita ce ta haifi wannan jamhuriyya ta 4 a wannan kasa don haka ita ce rana mafi cancanta a kira ranar dimokuradiya. Ware wannan rana kuma ya tabbatar da cewa har duniya ta tashi ‘yan Nigeria ba za su manta da cin zarafin da Babangida ya yi wa miliyoyin masu kada kuri’a wajen soke zaben shugaban kasa na 1993 ba. Har abada Yarbawa ba za su manta da cewa akwai ‘yayan kunama da ba su san halacci ba(Irinsu Obasanjo) da kuma ‘yayan goyo da suka san su yi halacci (irinsu Buhari).

Exit mobile version