Rabiu Ali Indabawa" />

Rasha Na Zaben Raba-gardama Kan Tsawaita Mulkin Putin

December 26, 2017 - Moscow Region, Russia - Russia's president VLADIMIR PUTIN at an informal summit of CIS heads of state at the Novo Ogaryovo residence. (Credit Image: © Sharifulin Valery/TASS via ZUMA Press)

Al’ummar Rasha na zaben raba gardama game da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska, matakin da zai bai wa shugaban kasar bladmir Putin damar zarcewa kan karagar mulki har zuwa shekara ta 2036.

Tuni jami’an tsaro suka dukufa wajen hana cinkoson jama’a a yayin zaben don hana bazuwar cutar Korona, yayin da zaben zai kai har zuwa ranar Laraba mai zuwa.

Mahukuntan kasar sun tanadi kyallayen rufe baki da hanci  da sabulun wanke hannu da mutane kimanin miliyan 110 za su yi amfani da su a yayin kada kuri’unsu a yankuna 10 na kasar.

Masu aikin rarraba kayayyakin zaben, su ma sun sanya safar hannu duk dai da nufin gujewa kamuwa da cutar Korona.

Hukumomin Rasha su zakuda da zaben ne daga 22 ga watan4 da ya gabata zuwa wannan lokaci saboda fargaban cutar Korona.

A watan Junairu shugaba Putin ya bullo da tsarin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, kuma Majalisun Dokokin kasar ba su yi wata-wata ba wajen amincewa da matakin.

Exit mobile version