Mataimakin shugaban kungiyar al’ummar Zabarmawa ta Nijeriya reshen Jihar Kogi, Mallam Umar Faruk Bin Imam Umar ya bayyana cewa rashin aikin yi a tsakanin matasa ne silar tabarbarewar tsaro a Nijeriya.
Mallam Umar ya bayyana hakan ne lokacin da yake hirarsa da wakilimmu a garin Lakwaja, babban birnin Jihar Kogi a ranan Talatan da ta gabata.
Ya bayyana rashin jin dadinsa duba da yadda matsalar tsaro ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma tare da neman gurgunta tattalin arziki da kuma zamantakewar kasar nan, sannan ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da kamfanoni masu zaman kansu da su samar wa da ‘yan kasa, musamman matasa abin yi domin magance zaman kashe wando a tsakaninsu, wanda yin hakan, a cewarsa zai taimaka wajen kawo karshen kalubalen tsaro da Nijeriya ke fuskanta a yanzu.
Ya ce, “A matsayina na shugaban al’umma zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira da babban murya ga gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi har da kamfanoni masu zaman kansu da su samar wa al’umma musamman matasa aikin yi, domin rage zaman banza a tsakaninsu.
“A ganina yin haka zai yi matukar tasiri wajen magance kalubalen tsaro da kasar nan ke fama da ita a halin yanzu,” in ji shi.