Dan wasan gaba kuma kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi ya bayyana cewar rashin barin Barcelona da bai yi ba a bana ya shafi rashin kokarin da yake fuskanta a kwallo kawo yanzu.
A cikin watan Agustan shekarar nan, kyaftin din Argentinan ya bukaci barin Barcelona zuwa wata kungiyar don ci gaba da buga wasa sai dai Barcelona ba ta bar dan wasan ya motsa ba, inda ta bukaci a biya fam miliyan 624, kudin da aka gindaya ga duk kungiyar da ke son daukar Messi idan yarjejeniyarsa bai kare a Camp Nou.
Messi ya bayyana cewar ya yi iya kokarin da zai yi don barin kungiyar tun fara kakar bana kamar yadda ya shaidawa gidan talabijin La Sedta a Spaniya sai dai kungiyar ta hanashi tafiya kuma hakan ya shafi kokarinsa.
“A gaskiya yanzu ina cikin farin ciki, amma a wancan lokacin na shiga hali mai muni kuma a wannan lokacin ina jin dadi sosai kuma a shirye nake na fuskanci kowanne kalubalen da ke gabanmu.” In ji Messi
Ya ci gaba da cewa ”Na san da cewar muna cikin mawuyacin hali a wannan lokacin tun daga jagoranci da rawar da muke takawa a fili, amma ina cike da murna kuma ina fatan nan gaba komai zai koma daidai.”
Kwantiragin Messi zai kare a karshen kakar wasan bana, zai kuma iya tattaunawa da wasu kungiyoyin tun daga 1 ga watan Janairu amma shugaban Barcelona na rikon kwarya, Carlos Tueskuets ya fada cewar idan ana batun matsin tattalin arziki ya kamata su sayar da Messi ga wata kungiyar.
Cikin watan Oktoba Mario Bartomeu ya yi murabus daga shugaban Barcelona, kuma cikin watan Janairu ake sa ran zaben wanda zai ja ragamar kungiyar sannan a cikin watan Nuwamba ne ‘yan wasan Barcelona suka cimma yarjejeniyar rage albashi, sakamakon matsin tattalin arziki da cutar korona ta haddasa.